Kun ci amanar Sardauna - Gwamna Yahaya Bello ya caccaki dattawan arewa

Kun ci amanar Sardauna - Gwamna Yahaya Bello ya caccaki dattawan arewa

- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya caccaki dattawan arewa inda ya zargesu da mayar da yankin baya a maimakon tabbatar da ci gabanta

- Bello ya ce shugabannin yankin da suka zo bayan Ahmadu Bello sun ki dorawa daga inda ya tsaya

- Ya zargi shugabannin da kunna wutar rikici na kabila da addinai wanda ya hana yankin zaman lafiya tare da kawo zubar jini

A ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya caccaki dattawan arewa inda ya zargesu da mayar da yankin baya a maimakon tabbatar da ci gabanta.

Da yake magana a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin gidauniyar tunawa da Ahmadu Bello karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Bello ya ce shugabannin yankin da suka zo bayan Ahmadu Bello sun ki dorawa daga inda ya tsaya.

Gwamna Bello ya zargi shugabannin da kunna wutar rikici na kabila da addinai wanda ya hana yankin zaman lafiya tare da kawo zubar jini.

Ya ce duk da yankin ta samar da manyan masu kudi, har yanzu yankin ne koma baya saboda yadda jama'ar suka ki saka hannun jari tare da shigewa gaba ta bangaren kawo ci gaba.

Kun ci amanar Sardauna - Gwamna Yahaya Bello ya caccaki dattawan arewa
Kun ci amanar Sardauna - Gwamna Yahaya Bello ya caccaki dattawan arewa Hoto: The Cable
Asali: UGC

A don haka ya yi kira ga dattawan yankin da su yi koyi da hallayar Sardauna don ci gabanta.

"Marigayi Ahmadu Bello yana nuna daidaito da rashin boye-boye a shugabancinsa.

"A saboda haka ne ya samu ci gaba mai tarin yawa sannan ya kafa martabar jama'ar arewa a idon duniya.

"A takaice, rashin gaskiya a tsakanin shugabannin yankin ya zama babban matsala wurin hana ci gaban yankin. Yadda za a shawo kan matsalar shine koyi da nagartar Sardaunan Sokoto wanda ya yi watsi da kabilanci ko banbancin addini," yace.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta hana belin Wadume, ta garkame shi a gidan yari

Ya yi misali da mulkinsa wanda ke koyi da nagartar Sardauna wurin aiwatar da al'amuransu.

Ya ce: "Jihar Kogi bata aminta da kabilanci ba."

Tun farko, Sanata Shekarau ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda fyade ya yawaita da sauran cin zarafin jinsi a fadin kasar nan.

Ya yi kira ga majalisun jihohi da su dauki manyan matakai wajen ladabtar da masu aikwata ire-iren laifukan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel