FG ta bayyana ranakun da jirage za su fara tashi da sauka a Kano, Legas da Abuja

FG ta bayyana ranakun da jirage za su fara tashi da sauka a Kano, Legas da Abuja

A cigaba da sassauta dokar kulle da rufe zirga - zirga a tsakanin kasa da kasa da kuma jihohin cikin kasa, gwamnatin tarayya ta sanar da dawowar tashi da saukar jirage a wasu manyan filayen jiragen sama na kasar nan.

A cikin wata sanarwa da ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya fitar da yammacin ranar Laraba, ya ce jirage za su fara tashi da sauka a iya cikin gida Najeriya a Abuja, Legas, Kano, Fatakwal, Owerri da Maiduguri.

A cewar Sirika, jirage za su fara tashi a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas da filin jirgin sama na Nmamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar 8 ga watan Yuli, 2020.

Filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano da filin jirgin sama na Fatakwal a jihar Ribas da na Maiduguri a jihar Borno za su fara aiki daga ranar 11 ga watan Yuli.

Sauran filayen jirgin sama na kasa za u koma aiki daga ranar 15 ga watan Yuli, kamar yadda ministan ya bayyana.

Kazalika, Sirika ya ce za a sanar da ranar dawowar tashi da saukar jiragen kasa da kasa nan gaba, ya bukaci jama'a su kara hakuri.

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta sake fitar da jerin wasu matakan sake sassauta dokar kulle a fadin Najeriya.

DUBA WANNAN: Gwamnan Bauchi ya dakatar da shugaban karamar hukuma, mataimakinsa da sakatare

Daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka akwai umarnin bude makarantun firamare da sakandire domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar rubuta jarrabawa kammala karatu.

Kazalika, gwamnatin tarayya ta janye dokar dakatar da zirga - zirgar mutane da ababen hawa a tsakanin jihohi.

Tuni aka bude manyan tashohin mota domin jigilar mutane da kayayyaki a tsakanin jihohi bayan dawowar harkokin sufuri ta motoci wacce aka shafe kusan wata uku da takatarwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel