Atiku ya bukaci FG ta shawo kan matsalar tsaro don ceton noma

Atiku ya bukaci FG ta shawo kan matsalar tsaro don ceton noma

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shawo kan matsalar tsaro da ya addabi yankin arewacin kasar

- Atiku ya jadadda cewa ta hakan ne kawai harkar noma zai daidaita a kasar

- Ya kuma yi kira ga 'yan kasa da su shirya kansu sannan su zuba ido wurin gano kaiwa da komowar 'yan ta'adda a yankunansu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shawo kan matsalar tsaro da ya addabi yankin arewa ta yadda noma zai dawo.

A wata takarda da Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce idan har ba a shawo kan matsalar tsaro ba, ta yuwu hakan ya zama babbar matsala ga kasar baki daya.

Atiku ya bukaci FG ta shawo kan matsalar tsaro don ceton noma
Atiku ya bukaci FG ta shawo kan matsalar tsaro don ceton noma Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Kamar yadda yace, "Noma ba wai aiki kadai bane ga mafi yawan jama'ar kasar nan, illa ya kuma kasance sana'a ce da ke jinin dukkan 'yan arewa.

"Noma da arewa abu daya ne. Amma rashin tsaron da yankin ke fama da shi yana kawo cikas ga harkar noma.

"A don haka nake kira ga gwamnatin tarayya da ta hada kai da jihohin da ke yankin don shawo kan matsalar tsaro. Rashin shawo kan matsalar tsaro zai iya zama matsalar da dukkan kasar nan za ta koka a kai."

KU KARANTA KUMA: Jihohi masu talauci: Tambuwal ya yi watsi da rahoton NBS

Atiku ya kara da kira ga 'yan kasa da su shirya kansu sannan su zuba ido wurin gano kaiwa da komowar 'yan ta'adda a yankunansu.

"Wuya bata kisa, za mu ga karshen wannan kalubalen," yace.

A wani labari na daban, tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya kushe gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan rashin tsaron da ya addabi yankin arewa.

Ya bayyana gwamnatin a matsayin mafi muni da aka taba yi a tarihin kasar nan.

A yayin jawabinsa a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya, Dalung ya ce duk da makuden kudin da ake warewa tsaro, babu abinda ya sauya a kan kashe rayukan 'yan Najeriya tamkar dabbobi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel