Kuma dai: Makarantun yara da makarantun firmare za su cigaba da zama a rufe - FG
Gwamnatin tarayya ta ce za a cigaba da rufe makarantun kananan yara da makarantun firamare da ke fadin kasar nan.
A sanarwar da ta fito kafin wannan, gwamnatin tarayya ta ce za a bude makarantu daga matakin firamare zuwa sakandire domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar rubuta jarrabawa.
Sai dai, a cikin wata sanarwa da Dakta Sani Aliyu, jagoran kwamitin yaki da annobar korona a kasa, ya fitar a Abuja ya ce ba za a bude makarantun kananan yara da makarantun firamare ba.
"Ba za a bude makarantun kananan yara da makarantun firamare ba har sai sanarwa ta gaba," a cewarsa.
A baya Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu a fadin kasar nan.
Hakan ya biyo bayan taron da ya wakana tsakanin kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa (PTF) da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
DUBA WANNAN: EFCC: Kotu ta fara shirin janye belin tsohon Sanata Shehu Sani
Kamar yadda gwamnatin tarayyar ta bayyana, azuzuwan da za su koma bakin karatun sun hada da:
1. Aji shida na dukkan makarantun firamare.
2. Daliban aji uku da na aji shida na makarantun sakandaren da ke fadin kasar nan.
Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka ba.
Gwamnatin tarayyar ta kara da amincewa da sauka ta tashin jiragen sama a cikin fadin kasar nan kadai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng