Sabon shugaban APC, Mai Mala Buni, ya isa hedikwatar APC domin gudanar da taro na farko

Sabon shugaban APC, Mai Mala Buni, ya isa hedikwatar APC domin gudanar da taro na farko

Sabon shugaban riko na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya isa hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa domin gudanar da taro na farko bayan rantsar da kwamitin da ya ke shugabanta a makon jiya.

Taron shine yunkurin Buni na farko na fara yin sulhu tare da samar da zaman lafiya a cikin jam'iyyar APC mai fama da rigingimun shugabanci a matakin kasa.

A makon jiya ne shugaban kwamitin rikon kwaryar shugabancin jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya karbi ragamar tafiyar da harkokin jam'iyya tare da daukan alkawarin tabbatar da adalci ga dukkan mambobin APC.

Bayan kammala taron NEC a fadar shugaban kasa, sabon shugaban ya wuce kai tsaye zuwa hedikwatar jam'iyyar APC tare da sauran mambobin kwamitinsa 13.

Jami'an tsaron da suka garkame hedikwatar APC sun bude kofar shiga bayan zuwan Buni da tawagarsa jim kadan bayan kammala babban taron jam'iyya a Villa.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis, 26 ga wata ne jami'an 'yan sanda suka rufe hedikwatar jam'iyyar APC tare da hana shugabannin jam'iyyar masu biyayya ga Oshiomhole shiga ofisoshinsu.

Sabon shugaban APC, Mai Mala Buni, ya isa hedikwatar APC domin gudanar da taro na farko
Mai Mala Buni
Asali: Original

Da yake tattaunawa da manema labarai a hedikwatar APC, Buni, wanda shine gwamnan jihar Yobe, ya ce: "jam'iyya za ta yi tafiya da kowa da kowa, musamman jagororin APC.

"Dukkan mambobin jam'iyyar APC sun bayar da gudunmawa wajen gina jam'iyyar, a saboda haka za mu yi tafiya da kowa.

"Na san jam'iyyar APC sosai, saboda na taba rike mukamin babban sakataren jam'iyya har sau biyu, ina bawa dukkan mambobin jam'iyyar APC tabbacin samun adalci saboda tamkar 'yan uwan juna mu ke.

DUBA WANNAN: 'Duk kanwar ja ce': Matasan arewa sun juyawa APC da PDP, sun bayyana shirinsu na 2023

"Ni dan cikin gida ne kuma na dawo ne domin warware rigingimun da jam'iyya ke fama da su, saboda idan ba mu warware wadannan matsaloli ba, matsalolin za su warware tubalin ginin jam'iyya.

"Babu wani kwamiti da ya ke da ikon da ya wuce na kwamtin NEC a cikin jam'iyya, a saboda haka babu mai ikon sauya hukuncin da NEC ta zartar."

Buni ya ce kwamitin NEC ya umarci dukkan mambobin APC su janye duk wata kara da suka shigar a gaban kotu dangane da rikicin da jam'iyya ke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel