Wanda ake zargi da bata jarirai a Jihar Nasarawa ya shiga hannun Dakarun NSCDC

Wanda ake zargi da bata jarirai a Jihar Nasarawa ya shiga hannun Dakarun NSCDC

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa jami’an hukumar NSCDC sun cafke wani matashi mai shekaru 27 da haihuwa, Ahmadu Yaro, wanda ake zargi ya yi lalata da jaririya mai watanni uku.

Wannan abu ya faru ne a wani kauye da ake kira Adogi, a karamar hukumar Lafia, jihar Nasarawa. A cikin wata guda, an yi wa kananan yara har shida fyade a kauyen Adogi.

Idan ba ku manta ba a ranar 27 ga watan Mayu, aka samu labarin cewa an yi wa wata karamar yarinya mai suna Rukayya Aliyu fyade. Wannan jaririya ba ta wuce kwanaki 90 a Duniya ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi yunkurin yin irin wannan lalata da wata jaririya mai watanni biyu da haihuwa. An kai wannan hari ne jim kadan bayan an yi lalata da Rukayya Aliyu.

An fahimci a kan yi amfani da irin wadannan kananan yara ne wadanda ba su wuce watanni uku zuwa shida da zuwa Duniya ba. Daga nan kuma a jefar da su a kusa da wata makaranta.

KU KARANTA: Wanda ta ke zargin Mawaki D’Banj da laifin fyade ta yi jawabi

Wanda ake zargi da bata jarirai a Jihar Nasarawa ya shiga hannun Dakarun NSCDC
Yaro a hannun Dakarun NSCDC Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Ana zargin cewa masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da-dama su na zama a wannan kauye. Haka zalika akwai malaman tsibbu da su ka shahara a jihar da su ke zaune a garin na Adogi.

Binciken da jaridar ta yi ya bayyana mata cewa akwai wasu miyagu a kauyen da ke yi wa irin wadannan mutane da su ka saba yin mummunan fyade farautar jarirai da za ayi amfani da su.

Babban jami’in NSCDC na jihar Nasarawa, Gidado Fari, ya ce za a gurfanar da Ahmadu Yaro a gaban kotu. Za a yi wannan ne da zarar an kammala binciken da ake yi a kan matashin.

Gidado Fari ya shaidawa ‘yan jarida a ranar Laraba cewa Yaro ya amsa laifinsa, tare da bayyanawa jami’an tsaro yadda ya yi wa wasu kananan yara biyar irin wannan danyen aiki.

Fari ya ce wanda ake zargin ya na ikirarin cewa ya na fama da tabin hankali, abin da ba a iya tabbatarwa ba tukuna. Ana zargin shi kadai ne ya ke addabar mutanen kauyen da fyade.

Wanda ake zargi da bata jarirai a Jihar Nasarawa ya shiga hannun Dakarun NSCDC
Yaro a hannun Dakarun NSCDC Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel