Kurunkus: Buhari ya fadi wanda ya amince da shi a matsayin shugaban APC na rikon kwarya

Kurunkus: Buhari ya fadi wanda ya amince da shi a matsayin shugaban APC na rikon kwarya

- Alamu na nuni da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da tsagin Victor Giadom a matsayin shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya

- Hakan ta bayyana ne bayan Giadom ya samu sahalewar shugaba Buhari domin kiran taron ma su ruwa da tsaki a gudanar da harkokin jam'iyyar APC (NEC)

- An tsayar da ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, domin gudanar da taron NEC a fadar shugaban kasa da ke Abuja

Tsagin shugabancin jam'iyyar APC da ke karkashin Mista Victor Giadom ya kira taron masu ruwa da tsaki a gudanar da harkokin mulkin jam'iyyar APC (NEC).

Za a yi taron ne ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo.

A cikin wani jawabi da Giadom ya fitar ranar Talata, 23 ga watan Yuni, ya ce ya kira taron ne bayan samun sahalewar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ya ce za a yi taron na NEC ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Wani bangare na sanarwar ya bayyana cewa, "ni, Cif Victor Giadom, bisa dogaro da tabbatar da ni da kotu ta yi a matsayin shugagaban APC na kasa da kuma samun sahalewar shugaba Buhari, ina gayyatar mambobin NWC da NEC zuwa babban taron jam'iyya wanda aka so gudanarwa tun ranar 17 ga watan Maris amma aka daga."

Giadom, dan asalin jihar Ribas, ya kasance mataimakin shugaban babban sakataren jam'iyya na kasa kafin ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya bayan kotu ta tabbatar da dakatar da Oshiomhole.

Giadom ya yi ikirarin cewa ya samu sahalewa da amincewar shugaba Buhari kafin ya kira taron NEC kamar yadda gwamonin APC suka nemi shugaban kasa ya bayar da umarnin a gudanar da taron domin warware rigingimun shugabanci da jam'iyyar APC ta tsinci kanta a ciki.

A ranar Litinin ne kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC (PGF) ta ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa domin sanar da shi matsayar mambobin kungiyar dangane da rigingimun da jam'iyyar APC ke fama da su a kasa.

Kurunkus: Buhari ya fadi wanda ya amince da shi a matsayin shugaban APC na rikon kwarya
Buhari yayin taron NEC
Asali: Twitter

Shugaban PGF kuma gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu, ne ya sanar da hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala ganawarsu da shugaba Buhari a fadarsa, Villa, da ke Abuja.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kubutar da leburori 600 da wasu Indiyawa suka kulle a cikin kamfani a Kano

Bagudu ya bayyana cewa suna goyon bayan shugaba Buhari domin ya kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a bullowa rigingimun shugabanci da suka dabaibaye jam'iyyar APC.

Gwamnan na jihar Kebbi ya na tare da takwarorinsa na jihar Filato; Simon Lalong, da na jihar Jigawa; Abubakar Badaru, yayin da ya ke wannan jawabi.

A cewar Bagudu, shugaba Buhari ya bawa gwamnonin tabbacin samun goyon bayansa a dukkan matakin da zasu dauka na dawo da zaman lafiya a cikin jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel