NBET: Ahmed ta yi watsi da matakin Ministar wuta, ta dawo da Amobi ofis

NBET: Ahmed ta yi watsi da matakin Ministar wuta, ta dawo da Amobi ofis

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, ta dawo da shugabar kamfanin saida wutar lantarkin Najeriya, Marilyn Amobi, wanda Ministan wuta, Saleh Mamman ya tsige.

A sabon nade-naden da Zainab Ahmed ta yi, wa’adin Marilyn Amobi a NBET zai kare ne a ranar 24 ga watan Yuli, 2020. Amobi za ta cigaba da rike kujerar babbar darektar kamfanin lantarkin.

Da ta ke jawabi a lokacin da ta kaddamar da sababbin shugabannin NBET, Ahmed ta ce gwamnati ta na kokarin maida sha’anin wutar lantarki a hannun ‘yan kasuwa, jaridar Punch ta rahoto wannan.

Ministar tattalin arzikin ce ta ke rike da kujerar shugabar majalisar da ke sa ido a kamfanin NBET, ta ce dole ayi maza wajen ganin karfin ikon harkar wutar lantarki ta bar hannun gwamnatin kasar.

Sau biyu Ministan wutar Najeriya, Saleh Mamman ya na sallamar Amobi daga NBET.

KU KARANTA: Amobi ta ki barin ofis bayan Ministan wuta ya tsige ta daga kujerar NBET

NBET: Ahmed ta yi watsi da matakin Ministar wuta, ta dawo da Amobi ofis
Ministar kudi, Zainab Ahmed Hoto: NES
Asali: UGC

Don haka Ahmed ta bukaci shugabannin da ke sa ido a kamfanin, su yi kokarin ganin an karkare wannan kokari na damka iko a hannun ‘yan kasuwa zuwa lokacin da wa’adinsu zai cika a ofis.

Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da matakin yi wa majalisar NBET garambawul. Hakan na zuwa ne makonnin biyu da Saleh Mamman ya nemi ya tsige Amobi.

Wadanda su ka shiga cikin majalisar kamfanin sun hada da Alexander Okoh wanda aka dauko daga hukumar BPP wanda ke da fiye da 80% na hannun jarin kamfanin saida wutar lantarkin.

Sauran darektoci marasa iko da Ministar ta nada a karkashin hukumar sun hada da Darektar hukumar DMO na kasa, Patience Oniha, sai kuma Darektan ofishin kasafin kudi, Ben Akabueze.

Tsohon shugaban hukumar NSE, Suleyman Ndanusa ya na cikin majalisar, haka zalika tsohon shugaban kungiyar NSE, Injiniya Mustapha Shehu, da Adeyeye Adepegba, sai ita Marylin Amobi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel