Rudani: Bayan APC ta jaddada Ajimobi, wani jigo a jam'iyyar ya sake bayyana kansa a matsayin shugaba

Rudani: Bayan APC ta jaddada Ajimobi, wani jigo a jam'iyyar ya sake bayyana kansa a matsayin shugaba

- Jam'iyyar APC ta fada cikin babban rudanin shugabanci biyo bayan dakatar da shugabanta, Adams Oshiomhole

- Mutane uku ne suke ikirarin shugabancin jam'iyyar na rikon kwarya a cikin sa'o'i 24

- Mataimakin shugban jam'iyyar APC na yankin kudu maso kudu, Hilliard Eta, ya fito ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa mai kula da yankin kudu maso kudu, Price Hilliard Eta, ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya.

Eta, dan asalin jihar Kuros Riba, ya ce ya karbi shugabancin jam'iyyar ne biyo bayan rudananin shugabanci da ake fama da shi a jam'iyyar APC bayan dakatar da shugabanta na kasa, Adams Oshiomhole.

Bayan ya sanar da kansa a matsayin shugaba, Eta ya nada gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a matsayin shugaban kwamitin zaben fidda 'yan takarar jihar Edo.

Har wa yau, ya sanar da kafa wata kwamitin daukaka karar zabe na mutum biyar karkashin jagorancin Farfesa Mustapha Bello da Dr Kayode Ajulo a matsayin sakatare.

Eta ya jadada cewa Victor Giadom baya cikin NWC tun lokacin da ya yi murabus domin takarar mataimakin gwamna a Rivers a babban zaben da ta gabata.

Rudani: Bayan APC ta jaddada Ajimobi, wani jigo a jam'iyyar ya sake bayyana kansa a matsayin shugaba
Hilliard Eta
Asali: Facebook

Kazalika, ya sanar da cewa kujerar Cif Victor Giadom, mataimakin sakataren jam'iyyar APC, ta zama ta mai rabo, za a nada wanda zai maye gurbinsa.

DUBA WANNAN: Katsina: Buhari ya aika sako ga masu zanga - zanga a kan rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa rikicin shugabanci da ake yi a jami'yyar All Progressives Congress, APC, mai mulki ya dauki sabon salo yayin da kwamitin zartarwa na jami'yyar ya jaddada Abiola Ajimobi a matsayin shugaban riko.

Uwar jam'iyyar ta yi watsi da Victor Giadom, inda ta ce baya cikin 'yan kwamitin zartarwar tun lokacin da ya yi murabus domin ya yi takarar kujerar mataimakin gwamna a jihar Rivers.

Mataimakin shugaban jami'yyar ta APC na kasa shiyar Kudu maso Kudu, Hilliard Eta yayin jawabin da ya yi wa manema labarai bayan Giadom ya bar sakatariyar jam'iyyar ya ce an fara shirin zaben fidda gwani na gwamnan Edo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel