Bayan ficewar gwamna Obaseki, APC ta sake rasa mataimakin gwamna

Bayan ficewar gwamna Obaseki, APC ta sake rasa mataimakin gwamna

- A ranar Talata ne gwaman jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC

- Sa'o'i kadan bayan sanar da ficewarsa, mataimakin Obaseki, Philiph Shaibu, ya sanar da cewa ya bi sahun maigidansa

- A ranar Juma'a ne APC ta sanar da cewa ta kori takarar da Obaseki ya ke kara nema a inuwar jam'iyyar saboda wasu matsaloli da aka gano a takardunsa na karatu

Philiph Shuaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, ya bi sahun maigidansa, gwamna Godwin Obaseki, wajen sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC.

Mista Shaibu ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC a ranar Talata.

Obaseki, ya sanar da yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar APC bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Obaseki ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban a ranar Talata, 16 ga watan Yuni.

Gwamnan ya yi furucin hakan ne a kan hanyarsa ta fita daga fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Yayin zantawarsa da manema labarai a fadar, Obaseki ya ce zai nemi takarar zango na biyu a wata jam'iyar ta daban.

Biyo bayan hana shi takara da uwar jam'iyar APC ta yi a ranar Juma'ar da ta gabata, Obaseki ya bayyana cewa zai yanke shawarar matakinsa na gaba bayan ya gana da Buhari.

Bayan ficewar gwamna Obaseki, APC ta sake rasa mataimakin gwamna
Obaseki, Oshiomhole da Shaibu
Asali: UGC

Shugaban kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyyar APC, Jonathan Ayuba, shi ne ya bayar da sanarwar haramtawa Gwamna Obaseki tsayawa takara tun gabanin zaben fidda gwani.

DUBA WANNAN: Ganduje ya goyi bayan APC a kan korar takarar Obaseki, ya yi magana a kan zaben Edo

Ayuba ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takara ne sakamakon matsalar da aka gano akwai a tattare da takardunsa na makaranta.

Akwai yiwuwar babu inda gwamna Obaseki zai jarraba sa'arsa ta tsayawa takarar gwamnan sai a karkashin inuwar jam'iyyar PDP bayan ya cika bujensa da iska daga jam'iyyar APC.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa, tuni jam'iyyar PDP ta fara zawarcin gwamna Obaseki yayin da uwar jam'iyyar APC ta huro masa wuta.

An dade ba a ga maciji tsakanin Gwamna Obaseki da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, wanda ya goyi bayansa a shekarar 2016.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel