Yanzu-yanzu: Majalisar jihar Niger ta yi wa gwamnan jihar kirar gaggawa

Yanzu-yanzu: Majalisar jihar Niger ta yi wa gwamnan jihar kirar gaggawa

Majalisar jihar Niger ta yi kiran gaggawa ga Gwamna Abubakar Sani Bello don yi musu bayanin dalilin da yasa gwamnatinsa ta kasa kawo karshen kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi a jihar.

'Yan majalisar sun ce tun a watan Nuwambar 2019, an samu hauhawar hare-hare a jihar. Sun kuwa zargin gwamnatin da kin yin komai a kai.

Har ila yau sun yi zargin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula a kan yaki da rashin tsaro.

Yanzu-yanzu: Majalisar jihar Niger ta yi wa gwamnan jihar kirar gaggawa
Yanzu-yanzu: Majalisar jihar Niger ta yi wa gwamnan jihar kirar gaggawa Hoto: Thisday
Asali: UGC

'Yan majalisar jihar sun kara da kiran gaggawa ga kwamishinan 'yan sandar jihar tare da umartarsa da ya sauya wa dukkan DPO na yankunan wurin aiki. Sun yi ikirarin cewa babu abinda suke yi don yaki da rashin tsaro a yankunansu.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukuma a Adamawa

A gefe guda mun ji cewa a ranar Juma'a da ya gabata ne 'yan bindiga suka harbe jami'an 'yan sanda biyu har lahira a kauyen Kusasu da ke yankin Erena na karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

An gano cewa 'yan sandan da suka hada da sifeta tare da kofur na tsaron wurin samar da wutar lantarki a Shiroro da ke kan hanyar kauyen Kauore da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna.

'Yan sandan na aiki ne a ofishin 'yan sanda da ke Zumba kuma sun yi musayar wuta tsakanin su da 'yan bindigar.

Duk da 'yan sandan sun yi nasarar bai wa Injiniyoyin kariya, amma sun rasa rayukansu sakamakon raunikan da suka samu daga harbin bindiga.

Kamar yadda majiya mai karfi da ke kusa da kauyen ta sanar, an kashe daya daga cikin 'yan bindigar amma kuma an rasa 'yan sandan biyu saboda rashin yawansu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun ya ce 'yan sandan biyu sun bace sakamakon musayad wuta da suka yi da 'yan bindiga a kauyen Kusasu da ke karamar hukumar Shiroro.

Amma kuma yace an tura jami'an tsaro don ceto 'yan sandan. Ya bada tabbacin cewa za su damke 'yan bindigar babu jimawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel