COVID-19: Tsabar yunwa ta sa mu fashi da makami - Matasa masu fashi

COVID-19: Tsabar yunwa ta sa mu fashi da makami - Matasa masu fashi

Matasa masu nishadantarwa sun shiga hannun hukumar 'yan sanda karkashin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami sakamakon zargin su da ake da laifin fashi da makami.

Sun sanar da rundunar cewa yunwa da rashin abinci ne ya tilasta su fada wa harkar fashi da makami bayan saka kullen dakile yaduwar muguwar cutar korona.

Daya daga cikinsu mai suna Michael Chinonso mai shekaru 25 mawakin gambara ne yayin da Victory Chimelu mai shekaru 22 yake waka. An damke su a ranar Laraba da ta gabata tare da wasu mutum biyar da ake zargi a wani gida a Legas.

An gano cewa matasan sun bukaci siyan waya kiran iPhone 11 a wani shagon yanar gizo mai suna Jiji.com a ranar 10 ga watan Afirilun 2020 a kan farashin N450,000.

Bayan karbar wayar daga wurin wakilin shagon mai suna Anifowoshe Itunu, ya tura mishi sakon kudi na bogi amma sai suka hadu da Chimelu suka daure shi.

COVID-19: Tsabar yunwa ta sa mu fashi da makami - Matasa masu fashi
COVID-19: Tsabar yunwa ta sa mu fashi da makami - Matasa masu fashi Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Daga nan sai suka siyar da wayar ga wani da ke Ogba a Ikeja a kan N350,000 wanda aka tura asusun bankin Chinonso.

'Yan sandan sun ce matasan sun sanar da cewa wannan ne karo na uku da suka siyar da waya kirar iPhone 11 Pro Max yayin kullen korona. Sun ce sauran biyun sun siyesu ne a yanar gizo da katin ATM na sata.

KU KARANTA KUMA: Tsaro: APC ta yi wa PDP raddi a kan bukatar murabus din Masari

Jaridar Daily Trust ta gano cewa Chinonso ya yi yunkurin tserewa ta hanyar haura bene tsirara amma sai 'yan sanda suka damke shi tare da kai shi asibiti saboda ciwukan da yaji.

A ikirarinsu, Chinonso da Chimelu sun ce suna waka a wata mashaya da ke Legas da dare. Amma saboda kulle da yunwa ne yasa suka fada wannan harkar.

"A yayin kullen, babu abinda za mu ci na kusan sati biyu. Tuni mutane suka fara bin mu bashi. Bamu da hanyar samun kudi a yayin kullen nan," suka ce.

Wadanda ake zargin sun ce suna taba damfarar yanar gizo baya ga waka da suke yi.

A yayin tsokaci a kan wannan ci gaban, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya ce yanar gizo babban ci gaba ne amma rundunarsa ba za ta lamuncewa 'yan ta'adda ba su gurbata ta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel