‘Dan Majalisar Borno Ya Ba ‘Yan Takaran APC Gudunmuwar Naira biliyan 1 a Yi Kamfe

‘Dan Majalisar Borno Ya Ba ‘Yan Takaran APC Gudunmuwar Naira biliyan 1 a Yi Kamfe

  • Muktar Betara Aliyu ya ware Naira biliyan 1.06 domin tallafa wa 'yan takarar APC da masu barin majalisa a jihar Borno
  • Zai ba 'yan takarar majalisar tarayya Naira miliyan 50, su ma masu takara a majalisar jiha za su samu Naira miliyan 20
  • Masu sharhi kan siyasa sun bukaci a binciki tushen kudin, wasu suna ganin irin wannan kashe-kashe sayen kuri’a ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Borno - ‘Dan majalisar wakilai ta tarayya, Muktar Betara Aliyu, ya sanar da ware zunzurutun kudi har Naira biliyan 1.06 domin cin zabe.

Muktar Betara Aliyu ya tanadi kudin don taimaka wa 'yan takarar jam'iyyar APC da 'yan majalisar da ke barin mukamansu a jihar Borno.

‘Dan majalisar Borno
Hon. Muktar Betara tare da Shugaban kasa a Aso Rock Hoto: @honbetara1
Source: Twitter

Hon. Muktar Betara ya yi rabon tallafin kamfe

Betara, wanda ke wakiltar mazabar Biu/Bayo/Shani/Kwaya Kusar a majalisar wakilai, ya bayyana tallafin ne ranar Lahadi in ji Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya saka ranar shiga Gombe don fara kamfen da gaske

Ya shaida cewa zai ba da wannan gudumuwa ne yayin bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben APC na jihar Borno a Maiduguri.

Yadda Betara ya kasa wa 'yan majalisa N1bn

Babban ‘dan majalisar ya ce za a ba 'yan takara 10 da kuma kowane ‘dan Majalisar Wakilan Tarayya da wa'adinsa yake karewa Naira miliyan 50

Zai kashe Naira miliyan 500 kan ‘yan takaran na APC da wadanda aka doke a zaben tsaida gwani.

Haka kuma, ya ce za a ba 'yan takara 28 da kowane daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Borno da wa'adinsa ke karewa Naira miliyan 20.

A nan ma Hon. Betare zai kashe wa abokan siyasa nasa na jihar Borno Naira miliyan 560.

Meyasa 'dan majalisar ya yi rabon kudin?

Hon. Betara ya bayyana cewa manufar hakan shi ne karfafa tsarin jam'iyyar da wayar da kan al'umma domin samun goyon bayan masu kada kuri'a.

Kara karanta wannan

Shugaban jam’iyyar APC da aka yi garkuwa da shi a Kano ya tsira bayan kwanaki 68

Ya bukaci shugabannin jam'iyyar da su koma ga jama'a a matakin mazabu da kananan hukumomi, su nemi afuwarsu tare da barar kuri’unsu a 2027.

Betara kwararren akawu ne, kuma ya fara zama dan majalisar wakilai a shekarar 2007. Tun daga lokacin ya samu nasarar lashe zabe a jihar Borno.

Ya taba shugabantar kwamitoci daban-daban a majalisar, ciki har da kwamitin soji, tsaro da kasafin kudi.

Jama'a sun bukaci a binciki tushen kudin

Sai dai wannan tallafi na Naira biliyan 1.06 ya jawo tambayoyi daga wajen masu sharhi kan siyasa, musamman game da inda kudin suka fito.

Wani masani kan harkokin siyasa, Dr Lawan Cheri, ya ce babu laifi idan mutane suka tambayi inda dan majalisar ya samo makudan kudin nan.

Cheri ya ce musamman idan aka yi la'akari da albashi da alawus-alawus din da 'yan majalisa ke karba, babu laifi a ji daga ina dukiyar ta fito.

Masanin ya yi gargadin cewa wasu 'yan siyasa kan ba masu takara gudumuwa da sa ran za su fanshe daga baya idan an kafa gwamnati.

Kara karanta wannan

Sakon Tinubu ga shugaban Nijar, Tchiani bayan rasuwar mahaifinsa

A cewar Dr. Cheri, hakan na iya haifar da cin hanci da rashawa, tare da hana al'umma samun ayyukan more rayuwa da suka kamata.

An yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta sanya ido kan irin wadannan daruruwan miliyoyi da 'yan siyasa ke batar wa a yanzu.

Shi ma wani masani kan harkokin jama'a, Dr Alhaji Ahmadu Ibrahim, ya bukaci hukumomin da abin ya shafa su binciki kashe-kashen kudin.

Ahmadu ya ce irin tallafin nan na Naira biliyan daya da dan majalisa ya bayar ya kamata ya jawo hankalin hukumomi su binciki tushen kudin.

‘Dan majalisar Borno
Kashim Shettima da ‘dan majalisar APC a Borno, Muktar Betara Hoto: @honbetara1
Source: Twitter

Wadanda suka ki karbar mukami wajen Tinubu

Ku na da labari akwai wasu 'yan siyasa da fitattun mutane da shugaban kasa ya nemi ya ba su matsayi amma suka ki karba.

Cikin wadanda suka ki karbar mukami daga wajen Bola Tinubu har da Ayodele Fayose, Fatima Alkali da kuma Sanata Orji Uzor Kalu.

Fatima Alkali wata farfesa da aka nemi a sa ta cikin hukumar NLRC amma ta ce sai dai a kai kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng