COVID-19: Ka rika tuntubar mu, ka dena bamu umarni - Malaman addinai ga El-Rufai

COVID-19: Ka rika tuntubar mu, ka dena bamu umarni - Malaman addinai ga El-Rufai

- Malaman addinin Musulunci karkashin inuwar United Muslim Foundation ta yi taro a Zaria a ranar Alhamis

- Yayin zantawa da manema labarai bayan taron, shugaban JIBWIS na jihar ya yi kira ga gwamnan da ya dinga tuntubarsu kafin yanke hukunci

- Sheikh Tukur Isa ya ce Gwamna El-Rufai bai taba tuntubarsu ba yayin yanke hukunci a wannan annobar, sai dai su samu umarni

Malaman addini karkashin inuwar United Muslim Foundation (UMS), a ranar Alhamis sun yi taro a Zaria don sake duba sharuddan dage dokar kulle a jihar Kaduna.

A yayin zantawa da manema labarai bayan taron da aka yi a cibiyar matasa da ke Tudun Wada, Zaria, Malam Tukur Isa, shugaban JIBWIS na jihar, ya ce sun amince da sharuddan.

Ya kara da cewa: "Amma kuma muna son yin amfani da wannan damar wurin sanar da gwamna cewa malaman addini ne ke da hakkin sanar da matsayarsu a fannin addini yayin annoba.

"A don haka, rashin mutuntawa ne a dinga bai wa malaman addini umarni wadanda suke wakiltar.

"A wannan lokacin na kulle, gwamnan yana kiranmu ne kawai ya bamu umarni kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana. Ba a taba tuntubarmu ba sai dai a bamu umarni.

COVID-19: Ka rika tuntubar mu, ka dena bamu umarni - Malaman addinai ga El-Rufai
COVID-19: Ka rika tuntubar mu, ka dena bamu umarni - Malaman addinai ga El-Rufai. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Fyade: An yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya

"A matsayinmu na malamai, ya kamata gwamnan ya nemi sanin hukunce-hukunce a kan wasu al'amura.

"Muna sanar da wannan ne don gwamnan ya dinga mutunta matsayarmu wacce ita ce wakilcin addini."

A dayan bangare, shugaban kungiyar, Malam Rabi'u Abdullahi, ya yi kira ga gwamnan da ya bude kasuwanni da makarantu don rufe su na ci gaba da matsantawa jama'ar jihar.

Abdullahi ya yi kira ga mazauna jihar da su tuba daga zunubbansu. Ya ce annobar Coronavirus ta samo asali ne daga zunubban mutane.

Idan za mu tuna, Gwamna El-Rufai a ranar Talata ya dage dokar kulle a jihar wacce ta kwashe kwanaki 75 tana aiki a don dakile yaduwar annobar Coronavirus.

Dage dokar a jihar ya bada damar bude wuraren ibada da bauta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel