An kori Janar a rundunar soji saboda sukar shugaban kasa

An kori Janar a rundunar soji saboda sukar shugaban kasa

Janar Ahmat Koussou Moursal ya rasa aikinsa a rundunar sojin kasar Chadi bayan ya soki shugaban kasar Chadi a cikin wata wasika da ya rubuta.

Gwamnatin kasar Chadi ta ce korarren Janar din ba zai samu kudin fansho ba balle garatuti. Gwamnatin ba ta bayar da wani dalili na daukan wannan mataki.

A cikin wasikar da ya rubuta, Janar Moursal ya yi zargin cewa shugaba Deby ya watsar da tsofin abokan aikinsa sojoji da ke garin Guera a yankin kudu maso gabas na kasar Chadi.

Babban sojan ya kara zargin gwamnatin Deby da kin biyan kudaden diyya ga wasu jama'a da gwamnatin tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre, ta ci zarafinsu.

Dokoki da tsarin aikin soji, a kusan ko ina a fadin duniya, basu bawa soja 'yanci da damar yin korafi a kan shugabanni a fili ba.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce zata bi diddigin mayakan kungiyar Boko Haram/ISWAP da 'yan bindigar Katsina da Sokoto duk inda suke tare da hallakasu.

A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta, rundunar soji ta ce ranta ya baci da harin da 'yan Boko Haram/ISWAP suka kai tare da kashe mata da kananan yara a kauyen Faduma Koloram da ke yankin karamar hukumar Gubio a jihar Borno.

An kori Janar a rundunar soji saboda sukar shugaban kasa
Idriss Deby a dajin Sambisa
Asali: Twitter

"Tuni an tura rundunoni zuwa yankin domin kashe wadanda suka kai harin ko kuma a kamasu. Mun aika sakon gaggawa zuwa ga kwamandan rundunar atisayen Ofireshon Lafiya Dole a kan a tsaurara matakan tsaro a yankin domin kare rayukan jama'a.

"Kazalika, rundunar soji tana sane da al'amuran 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma, musamman a jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara.

"Mun fuskanci cewa wasu daga cikin 'yan bindigar da aka fatattaka daga Katsina sun yi kaura zuwa makwabtan jihohi tare da kai hari a kan fararen hula.

DUBA WANNAN: Tantance 'yan takara: Babu alamun za ai min adalci -Gwamna Obaseki ya bayyana tambayoyin da ya sha

"Mu na mika sakon jaje da ta'aziyya ga jama'ar Najeriya, musamman na jihohin Borno, Katsina, Sokoto da Zamfara.

Mu na masu baku tabbacin cewa ba zamu bari ba, sai mun kawar da dukkan 'yan ta'adda masu cutar da jama'a," a cewar jawabin; mai dauke da sa hannun kanal Sagir Musa, mukaddashin kakakin rundunar soji.

Rundunar soji ta ce zata hada kai da rundunar sojojin sama da sauran hukumomin tsaro a jihohin da ke fama da matsalolin domin a tabbatar da dawowar zamana lafiya, kamar yadda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni.

Kazalika, rundunar sojin ta bayar da tabbacin cewa ba zata bar irin wannan aikin ta'addanci ya cigaba da faruwaba ba tare da ta nuna fushinta a kan 'yan ta'adda ba, a ko ina suke a fadin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel