Sanatan APC ya bukaci a mayar da aikin majalisa na wucin gadi

Sanatan APC ya bukaci a mayar da aikin majalisa na wucin gadi

Sanata mai wakiltar mazabar jihar Borno ta yamma, Ali Ndume, ya yi kira a kan a mayar da aiyukan dukkan majalisun tarayya zuwa na wucin gadi domin rage albashin mambobinta da kashe kudin tafiyar da harkokin gwamnatin kasa.

Ndume ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Abuja ranar Laraba, inda ya kara da cewa ya kamata a rage albashin manyan ma'aikatan gwamnatin tarayya domin samun kudin da za a yi manyan aiyukan raya kasa.

"Ni a wurina babu wata matsala idan an mayar da aikin majalisa na wucin gadi da za a ke yi lokaci zuwa lokaci, a halin yanzu ma bama zama fiye da sau biyu ko uku a cikin sati.

"Idan majalisa ta koma aikin wucin gadi, tilas za a rage albashin mambobinta. Ba zai yiwu mu cigaba da tafiya a tsarin kashe kaso 70 na kasafin kudi a kan tafiyar da aikin gwamnati da ma'aikata ba.

"Ya kamata gwamnati ta rage albashin manyan ma'aikata. Misali, darekta da ke zaune a gida ba ya zuwa ofis, bai kamata a biyashi cikakken albashi ba.

Ndume, mamba a jam'iyyar APC, ya bukaci gwamnati ta bawa ma'aikata tallafi idan tana so su zama masu sadaukarwa da zasu rungumi ragin albashi.

Sanatan APC ya bukaci a mayar da aikin majalisa na wucin gadi
Sanata Ali Ndume
Asali: UGC

"Ya kamata gwamnati ta yi duba na tsanaki a kan kudaden da take kashewa a kan ma'aikata, wanda ke lashe kusan kaso 70% na kasafin kudi. Akwai bukatar a ingiza kudi domin kaddamar da manyan aiyukan raya kasa.

"Ya kamata mutane su kasance masu sadaukarwa. Wannan lokacine na sake duban al'amura da natsuwa.

"Sai dai, duk lokacin da na yi magana irin wannan, jama'a su kan fito su sokeni tare da kirana sunaye marasa dadi. Amma hakan ba zai hana na fadi ra'ayina ba.

DUBA WANNAN: Zanga - zanga ta barke a jihar Katsina a kan rashin tsaro

"Akwai bukatar sadaukarwa, musamman a bangaren ma'aikata. Ma'aikata basa zuwa aiki amma ana biyansu cikakken albashi, ana cigaba da kashe musu kudi kamar a lokacin da suke aiki.

"Akwai wani uzuri na cigaba da kashe kudi a kansu? idan mutum ba zai iya aiki a cikin annoba ba, sai a bashi tallafi, a rage masa albashi," a cewar Sanata Ndume.

Kazalika, Sanatan ya bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da aikin wasu ma'aikatu da hukumomi na wucin gadi domin samun damar tattala kudaden da za a yi amfani da su wajen yi wa talakawa aiki da samar musu da kayan more rayuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel