Yanzu Yanzu: Jihar Neja ta sassauta dokar kulle na korona

Yanzu Yanzu: Jihar Neja ta sassauta dokar kulle na korona

- Gwamnatin jihar Neja ta sassauta dokar kulle da ta saka sakamakon annobar korona a fadin jihar

- Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya sanar da hakan a yau Talata, 9 ga watan Yuni, yayinda ya karbi rahoton kwamitin COVID-19 a jihar

- Ya yi umurnin bude harkokin kasuwanci amma ya ce a ci gaba da rufe makarantu

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya sassauta dokar kulle da ya saka a jihar saboda gudun yaduwar annobar coronavirus.

A cewarsa, ana iya dawo da dukkanin ayyuka na kasuwanci amma dai makarantu su ci gaba da kasancewa a kulle.

Yanzu Yanzu: jihar Neja ta sassauta dokar kulle na korona
Yanzu Yanzu: jihar Neja ta sassauta dokar kulle na korona Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Ya kuma umurci ma’aikatan gwamnati da su ci gaba da kasancewa a gida illa wadanda ke ayyuka masu muhimmanci.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayinda yake karban rahoton kwamitin jihar kan samar da wurin gwajin kwayoyin cutar COVID-19 a gidan gwamnati da ke Minna, jaridar The Nation ta ruwaito.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya nuna damuwarsa da yadda mazauna jihar sa ke ta ke dokar nesa-nesa da juna don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Bello ya sanar da hakan ne yayin jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron mako-mako da yake yi da mambobin kwamitin yaki da cutar korona na jihar.

"Abin takaici ne yadda muka rufe iyakokinmu tsakaninmu da wasu jihohin amma kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Masu babura suna yawan kaiwa da kawowa wanda hakan ke nuna karantsaye ga dokar gwamnatin."

Gwamnan ya sanar da dokar hana aikin babura a jihar na makonni biyu yayin da duk sauran dokokin za su ci gaba da aiki na tsawon makonni biyun.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, yayin jaddada kokarin gwamnatin na bada kariya ga ma'aikatan lafiya da kuma 'yan kwamitin yaki da cutar na jihar, Bello ya tabbatar da cewa gwamnati za ta dauka mataki mai tsauri a kan harkar ma'aikatan lafiyanta.

Gwamnan ya yi kira ga jama'a da su kiyaye tsaftar kansu, zama nesa-nesa da juna, saka takunkumin fuska idan za a shiga jama'a da kuma gaggauta neman shawarar masana kiwon lafiya yayin da wata alamar cutar ta bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel