Babu wata rufa - rufa: APC ta like fom din 'yan takarar gwamnan jihar Edo 6 a allon bango

Babu wata rufa - rufa: APC ta like fom din 'yan takarar gwamnan jihar Edo 6 a allon bango

A cigaba da shirye - shiryen gudanar da zaben fidda dan takarar gwamna da zai tsaya a karkashin inuwar jam'iyyarta, APC ta like fom din 'ya'yan jam'iyyar 6 da su ka nuna sha'awarsu ta yin takara.

A wani sabon salo na nuna cewa babu wata rufa - rufa, APC ta like takardun bayanan dukkan 'yan takarar a wani allon bango da ke hedikwatar jam'iyyar.

Jam'iyyar APC ta tsayar da ranar 22 ga watan Yuni a matsayin ranar da zata gudanar da zaben cikin gida domin fidda wanda zai mata takarar kujerar gwamna a jihar Edo.

Har yanzu ba a cimma matsaya dangane da yanayin zaben fidda gwarzon dan takarar gwamnan APC na jihar Edo ba, lamarin da ke ci gaba da kawo cece-kuce.

A yayin da kwamitin zartarwa na uwar jam'iyyar APC ya aminta da salon zaben kato bayan kato, inda duk mai shaidar zama dan jam'iyya zai iya yin zaben dan takarar da yake so.

Magoya bayan Gwamna Godwin Obaseki ba su aminta da hakan ba. Sun fi son wakilan jam'iyyar su fito don yin zaben.

Babu wata rufa - rufa: APC ta like fom din 'yan takarar gwamnan jihar Edo 6 a allon bango
APC ta like fom din 'yan takarar gwamnan jihar Edo 6 a allon bango
Asali: Twitter

Gwamna Obaseki na ta rokon fadar shugaban kasa da ta soke hukuncin kwamitin zartarwar jam'iyyar.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

An gano cewa fadar shugaban kasar ta shiga halin tsaka mai wuya a kan wannan al'amari.

Baraka a kan yanayin zaben fidda gwanin ya kai ga zargin cewa bangaren shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, na tsananta yakin neman kada Obaseki.

'Yan takara biyar ne ke adawa da Obaseki su ne: Pius Odubu, Osagie Ize-Iyamu, Chris Ogiemwonyi, Matthew Iduoriyekemwen da Osabo Obazee.

Shugaban jam'iyyar APC na Edo ta tsakiya, Chief Francis Inegbeniki, wanda yake na hannun daman Adams Oshiomhole, ya tattara laifuka 50 na Obaseki wadanda sun isa su hana gwamnan zarcewa.

Ya ce da yawa daga cikin 'yan jam'iyyar ba su amince da Obaseki da mataimakinsa ba saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da shugaban jam'iyyar tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel