Cikin gaggawa: An tafi da mahaifin gwamnan Nasarawa asibiti, an yi wa fadarsa feshi

Cikin gaggawa: An tafi da mahaifin gwamnan Nasarawa asibiti, an yi wa fadarsa feshi

- An garzaya da Sarkin garin Gudi da ke karamar hukumar Akwanga na jihar Nasarawa, Sule Bawa zuwa asibiti cikin gaggawa sannan aka killace shi

- Basaraken ya kasance mahaifi ga Gwamna Abdullahi Sule

- An kuma tattaro cewa an yi wa fadar sarkin da gidan gwamnan feshi

Rahoto da ke zuwa mana ya nuna cewa an dauki Sarkin garin Gudi da ke karamar hukumar Akwanga na jihar Nasarawa, Sule Bawa zuwa asibiti cikin gaggawa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa an killace basaraken wanda ya kasance mahaifin gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.

Cikin gaggawa: An tafi da mahaifin gwamnan Nasarawa asibiti, an yi wa fadarsa feshi
Cikin gaggawa: An tafi da mahaifin gwamnan Nasarawa asibiti, an yi wa fadarsa feshi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wani mazaunin garin Gudi wanda ya nemi a boye sunansa ya ce Bawa “ya kamu da zazzabi sannan sai ya fara tari.

“Hakan ya yi sanadiyar kai shi zuwa sashi na musamman da ke asibitin kwararru na Dalhatu Araf Specialist Hospital (DASH) a Lafiya, a ranar Laraba.

“A ranar Alhamis, sai wata tawaga na hukumar lafiya suka yi wa fadar da gidan gwamnan feshi,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ba a tabbatar da abun da ya haddasa rashin lafiyar nasa ba, yayinda mutanen da ke yankinsa suka kai ziyarar ban girma a ranakun kasuwa.

Zuwa yanzu asibitin bata yi tsokaci ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu cif a jihar sakamakon annobar korona.

Gwamnan ya bada wannan sanarwar ne a lafiya yayin taro da kwamitin yaki da cutar na jihar ta gudanar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan jihar Katsina ya bude kasuwanni, ya umurci ma'aikata su koma bakin aiki

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, cike da alhini yake sanar da mutuwar mutum hudu wanda suka hada da dan majalisar jihar mai wakiltar Nasarawa ta yamma daga cikin mutum 90 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa, samfur 705 aka kai wa hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya tun bayan da aka fara gwajin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel