Tsige sarki Sanusi: Kotu ta mayar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano 5 da aka dakatar

Tsige sarki Sanusi: Kotu ta mayar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano 5 da aka dakatar

- Kotun tarayya ta warware hukuncin majalisar dokokin jihar Kano na dakatar da wasu mambobinta biyar

- An dakatar da mambobin ne sakamakon kaurewar rikici a zauren majalisar yayin da aka gabatar da kudirin neman tsige Sanusi II

- Alkalin kotun, Jastis Lewis Alagoa, ya ce dakatar da 'yan majalisar ya sabawa kundin tsarin mulki

Wata kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta soke hukuncin dakatar da mambobin majalisar dokokin jihar Kano 5 saboda sun nuna dawa da tsige tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

A ranar 15 ga watan Maris ne majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da mambobinta guda biyar bisa zarginsu da hannu a sace sandar ikon majalisa yayin sauraren kudirin neman bincike da tsige Sanusi II.

'Yan majalisar da aka dakatar sun hada da; Yau Gwarma mai wakiltar mazabar Kunci da Tsanyawa, Labaran Abdul Madari mai wakiltar mazabar Warawa, Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar Gezawa.

Ragowar sune; Mohammed Bello mai wakiltar mazabar Rimingado da Tofa, da Salisu Ahmed Gwangwazo mai wakiltar mazabar birnin Kano.

Tsige sarki Sanusi: Kotu ta mayar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano 5 da aka dakatar
Majalisar dokokin jihar Kano
Asali: UGC

Da ya ke zartar da hukunci a ranar Laraba, alkalin kotun, Jastis Lewis Alagoa, ya ce dakatar da 'yan majalisar ya sabawa kundin tsarin mulki.

DUBA WANNAN: Kotu ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin da ya kashe mahaifinsa

Alkalin kotun ya bukaci majalisar ta gaggauta janye dakatarwar tare da biyan 'yan majalisar dukkan albashi da alawus dinsu na tsawon lokacin da aka dakatar da su.

A ranar 16 ga watan Maris ne aka tsige Sanusi II bisa zarginsa da almudahana duk an samu hargitsi a majalisar dokokin jihar Kano bayan 'yan majalisar biyar sun hada kai tare da kalubalantar kudirin neman a tsige tsohon sarkin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel