Bai wa 'yan sandan bayanin bogi: Kotu ta yi watsi da shari'ar Dino Melaye

Bai wa 'yan sandan bayanin bogi: Kotu ta yi watsi da shari'ar Dino Melaye

Wata babbar kotu da ke Abuja ta yi watsi da karar da gwamnatin tarayya ta kai na Sanata Dino Melaye a kan zarginsa da ake yi da bai wa 'yan sanda bayanan bogi.

Sanata Melaye, wanda bai dade da barin wakilcin jihar Kogi ta yamma ba a majalisar tarayya, ya gurfana a gaban kotu a kan laifuka biyu da ake zarginsa da su.

Laifukan sun hada da ba wa 'yan sanda bayanan bogi.

A yayin yanke hukunci, Alkali Olasumbo Goodluck ya zartar da cewa masu gabatar da kara sun kasa bada shaidu gamsassu a kan laifukan.

Bai wa 'yan sandan bayanin bogi: Kotu ta yi watsi da shari'arsu Dino Melaye
Bai wa 'yan sandan bayanin bogi: Kotu ta yi watsi da shari'arsu Dino Melaye Hoto: BBC
Asali: UGC

A watan Afirilun 2017, an zargi Dino Melaye da ba wa 'yan sanda bayanan bogi game da shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Kogi na lokacin, Edward David Onoja.

An zargi Melaye da bada sunan Onoja, wanda a yanzu shine mataimakin gwamnan jihar, a matsayin shugaban wadanda suka yi yunkurin kashe shi.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Gwamnatin Katsina ta dage dokar takaita zirga-zirga

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa a karshen makon nan ne Sanata Dino Melaye ya fito ya ba Duniya labarin yadda ya tsallake tarkon wasu mutane da su ka yi yunkurin gann karshen rayuwarsa.

Dino Melaye ya ce an kai masa hari za a kashe shi ne a gaban makaramtar nan ta koyon aiki ta jihar Kogi watau Kogi Polytechnic a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu.

Melaye ya bada wannan labari ne a shafinsa na zumunta na tuwita @dino_melaye. Shararren ‘dan siyasar ya bayyana cewa Ubangiji ne ya tsaga masa gyadar doguwa.

“Na godewa Ubangiji da wannan rana. Yau ce ranar da masu kisan-kai su ka nemi rayuwata a gaban makarantar Kogi State Polytechnic.” Inji @dino_melaye a tuwita.

Fitaccen ‘dan adawar gwamnatin na APC mai-ci ya kara da cewa: “Maimakon su kashe ni, shugaban gungun miyagun, Saka ya mutu. Ubangiji ya cika Ubangiji."

Melaye ya cigaba da godiya, ya na kiran sunan Ubangiji da yarukan Hausa, Ibo da kuma Yoruba. Ya rubuta: “Oluwa seun. Chineke edima. Nagode Ubangijin Duniya.”

Ba wannan ba ne karon farko da Dino Melaye ya fito ya na cewa ana neman ganin bayan rayuwarsa. Kawo yanzu ‘yan sanda ba su tabbatar da wannan zance ba.

A 2017, Dino Melaye ya ce an harbi motocinsa lokacin da wasu tsageru su ka shigo gidansa da ke Ayetoro-Gbede a karamar hukumar Ijumu, jihar Kogi cikin tsakar dare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel