Bana cikin gwamnatin El-Rufai - Hadiza El-Rufai
- Hadiza Isma El-Rufai, matar Gwamna Malam Nasir El-Rufai ta bayyana cewa bata cikin tafiyar gwamnatin mijinta
- Kamar yadda matar gwamnan ta bayyana a shafinta na twitter, ta ce bata kiran kanta da matar gwamna duk da kuwa mijinta ne ke shugabantar jihar Kaduna
- Ta jaddada cewa bata cikin tafiyarsa don kuwa bata karba wata rantsuwa ba da za ta tabbatar da ita a matsayin mai wani ofishi a gwamnatin
Hadiza El-Rufai, matar gwamnan jihar Kaduna, ta ce bata cikin tafiyar gwamnatin mijinta.
A yayin magana a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, Hadiza ta ce sau da yawa tana nesanta kanta daga yin tsokaci a kan zantukan shugabanci da siyasa.
Kamar yadda ta sanar, ba kamar gwamnoni ba da sauran masu mulki da aka zaba, bata karkashin wani ofishi da tayi rantsuwa, don haka kai tsaye take bayyana matsayarta a kan al'amura da dama.
Kamar yadda ta kara da cewa, shafin ta na kafar sada zumuntar zamani tana koyar da yare ne da sauransu.
"Kun taba ganin na saka 'matar gwamna' a bayanai na? Shafina na koyon yare ne da sauran al'amura marasa nauyi. Bana wallafa a kan shugabanci da siyasa. Duk da ina auren gwamna, bana cikin gwamnatinsa. Ban yi rantsuwa ba," tace.
KU KARANTA: Hedkwatar tsaro ta aike sakon gaggawa ga jihohin Arewa na tsakiya da Arewa maso yamma
Wannan tsokacin nata ya zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a kan kisan da 'yan bindiga suka yi wa jama'a a yankin kudancin jihar Kaduna.
Matar gwamnan ta shiga kanun labarai a watan Afirilun da ya gabata, bayan zarginta da aka yi da goyon bayan dan ta Bello Rufai bayan tsokacin da yayi na nuna cin zarafi ga mahaifiyar wani a Twitter.
Daga baya Hadiza ta bada hakuri a kan wallafarta tare da jaddada cewa bata goyon bayan cin zarafi kowanne iri ne.
"Na ga yadda wallafa ta fito. Ina bada hakuri ga wadanda na saba wa. Ina sake jaddada cewa bana goyon bayan cin zarafi kowanne iri," ta wallafa.
A yau ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai yake cika shekaru biyar cif a karagar mulkin jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng