A karon farko: Jam'iyyar PDP ta jinjinawa Buhari a kan kokarin samar da tsaro

A karon farko: Jam'iyyar PDP ta jinjinawa Buhari a kan kokarin samar da tsaro

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Zamfara, ta bayyana gamsuwarta da yadda gwamnatin tarayya ke yakar 'yan bindiga da sauran miyagun mutane da ke jihar.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da sakataren jam'iyyar na jihar, Alhaji Hashimu Modomowa ya fitar tare da mika wa ga manema labarai a Gusau.

Jam'iyyar ta tsame kanta daga tsokacin da kwamishinan raya karkara, Alhaji Abubakar Abdullahi yayi.

A karon farko: Jam'iyyar PDP ta jinjinawa Buhari a kan kokarin samar da tsaro
A karon farko: Jam'iyyar PDP ta jinjinawa Buhari a kan kokarin samar da tsaro Hoto: Megafetch
Asali: UGC

Ya zargi gwamnatin tarayya da mayar da hankali a kan yaki da annobar Coronavirus fiye da matsalar 'yan bindiga.

Modomowa ya ce kalaman kwamishinan zai iya kawo tashin-tashina tsakanin jihar da gwamnatin tarayya.

Kamar yadda yace, gwamnatin tarayya tana matukar kokari wajen yakar 'yan bindigar da sauran matsalolin da suka addabi jihar.

"Wannan ya hada da samar da birged daga ta rundunar sojin Najeriya, kungiya ta 2017 ta tallafin gaggawa ta rundunar sojin sama karkashin Operation Hadarin Daji", yace.

Modomowa ya kara da mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya da ta amsa kiran su na farfado da hakar ma'adanai a jihar.

Ya ce hakan zai matukar taka rawar gani wajen rage yawan miyagun laifuka tare da samar da guraben ayyuka ga matasan jihar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Kano ta yi zazzafan martani a kan bidiyon cibiyar killacewa da ke yawo

Sakataren PDP din ya jaddada cewa gwamnatin da jama'ar jihar za su ci gaba da mika godiya ga gwamnatin tarayya wajen toshe barakar 'yan bindiga da shawo kan annobar Coronavirus.

A gefe guda, mun ji cewa yankin Dapchi, babban birnin karamar hukumar Bursari ta jihar Yobe ta zama kufai bayan harin da 'yan ta'adda suka kai wa jama'ar garin.

Da yawa daga cikin mazauna garin sun yi shagalin bikin sallah karama ne a daji da kauyuka makusanta sakamakon tsoron da ya shiga zukatansu.

Wani mazaunin garin wanda ya zanta da SaharaReporters ya ce, "Zan iya kirga yawan jama'ar da ke Dapchi. Ba mu da yawa. Mutane duk sun tsere don samun mafaka. Su kan shigo amma suna komawa maboyarsu."

A makon da ya gabata ne mayakan ta'addancin suka dinga kai hari garin Dapchi inda suka kurmushe asibiti da fadar hakimi.

A halin yanzu, an daina bin hanyar Dapchi zuwa Damaturu saboda tsoron harin 'yan Boko Haram.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel