Zan cigaba da girmama yarjejeniyar da mu ka kulla da tubabbun 'yan bindiga

Zan cigaba da girmama yarjejeniyar da mu ka kulla da tubabbun 'yan bindiga

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawallen Maradun, ya ce har yanzu yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatinsa ta kulla da 'yan bindiga a jihar ba ta daina aiki ba.

Matawalle ya ce zai cigaba da girmama yarjejeniyar da gwamnatinsa ta kulla da 'yan bindigar da su ka tuba.

Ya kara da cewa gwamnati za ta yi amfani da karfin doka a kan 'yan bindigar da su ka ki rungumar sulhu.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, yayin da ya ke jajantawa jama'ar wasu kauyuka a kan harin da 'yan bindiga su ka ki mu su a makon jiya.

Ya mika sakon jajen ne ga jama'ar kauyukan Unguwar Rogo, Karda, Bidda da Kajera a yankin karamar hukumar Tsafe da kauyen Kabaje a yankin karamar hukumar Kaura - Namoda.

A kalla mutane 10 aka kashe tare da raunata wasu da dama kafin daga bisani jami'an tsaro su kawo dauki yayin hare - haren.

A cewar Matawalle, "ina aiki ba dare ba rana, ko barci ba na iya samu, saboda na tattauna da jami'an tsaro da sauran ma su ruwa da tsaki.

"Mun samu tabbaci daga wurin shugabannin Fulani da su ka karbi tsarinmu na sulhu a kan cewa za su tattauna da 'yan bindiga ma su kunnen kashi domin nuna mu su muhimmancin rungumar sulhu.

Zan cigaba da girmama yarjejeniyar da mu ka kulla da tubabbun 'yan bindiga
Bello Matawalle
Asali: Twitter

"Duk da mun koma tebur domin cigaba da sulhu, hakan ba ya nufin cewa ba za mu yi amfani da karfi ba wajen kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu ba."

A cigaba da yaki da ta'addanci a jihar Borno, bataliyar sojojin rukuni na 7 a rundunar soji ta daya a atisayen ofireshon LAFIYA DOLE (OPLD) ta samu nasarar kai wasu hare - haren kwanton bauna a kan mayakan kungiyar Boko Haram da na takwararta ISWAP.

DUBA WANNAN: Hotunan Buhari yayin Sallar Idi cikin jam'i, ya sha 'selfie' da 'yayansa a cikin gida

Dakarun soji na cigaba da kaddamar da manyan hare - hare tare da samun galaba a kan 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram da ISWAP a karkashin atisayen KANTANA JIMLAN wanda shugaban rundunar soji, laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya kaddamar domin tsananta yaki da 'yan ta'addar.

A irin wadannan zafafan hare - haren da dakarun soji ke kaiwa, sun kai wani hari a wata maboyar 'yan ta'adda da ke kan hanyar zuwa Adzunge.

Ba a kama kowa ba yayin harin saboda 'yan ta'addar sun tsere bayan sun hango rundunar sojoji ta tunkaro kauyen.

Sojojin sun samu kayan amfanin 'yan ta'addar da su ka hada da babur guda biyu da wani babban injin nika nikan lausi, wanda aka fi sani da 'Lister'.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng