Jirgin sama dauke da fasinjoji fiye da 100 ya yi hatsari a Pakistan
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa wani jirgin sama dauke da fasinjoji 100 ya rikito a wani yanki a kasar Pakistan.
Hukumar kula da jiragen sama na kasar ta bayyana a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, cewa jirgin ya rikito ne a birnin Karachi na Pakistan, Aljazeera ta ruwaito.
Abdul Sattar Khokhar, kakakin hukumar jirgin sama ta kasar, ya ce jirgin ya taso ne daga Lahore.

Asali: UGC
Ya ce jirgin yana dauke da fasinjoji 99 da ma'aikatan jirgi takwas.
Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna hayaki ya turnuke sararin samaniya a wurin da jirgin ya fadi da ke rukunin gidaje da ke Karachi.
Ma'aikatan agajin gaggawa sun isa wurin da jirgin ya yi hatsari, inda ya lalata gidaje.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Ayade ya zubar da hawaye yayinda ya dauke wa marasa karfi biyan haraji
A wani labari na daban, mun ji cewa a ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu, 2020, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwar cewa ta tare jirgin sama na wani kamfani a kasar Birtaniya da ke aiki a sararin samaniyar kasar.
An kama jirgin ne ya na cigaba da daukar fasinjoji a daidai lokacin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta haramta tashi da saukar duk wasu jiragen sama a fadin Najeriya.
Minista Hadi Sirika ya ce jirgin kamfanin Flair Aviation na kasar Birtaniya ne aka samu da laifin saba doka. Ba a ba wannan kamfani damar daukar fasinja ba inji ministan jiragen saman.
Mai girma ministan watau Hadi Sirika ya ce: “An ba wannan kamfani damar tashi domin zirga-zirgar taimakon jama’a ne, amma abin takaici sai mu ka kamu su, su na daukar fasinjoji.”
Da alamu cikin fushi, sanata Hadi Sirika ya fitar da jawabi: “Wannan rashin sanin ciwon kan sauran jama’a ne! An tsare jirgin saman, ana kuma yi wa ma’aikatan ciki tambayoyi.”
Bayan haka, Sirika ya rubuta cewa za a hukunta kamfanin a dalilin jawo fushin hukumomin kasar da ya yi a wannan marra. “Akwai hukunci mai matukar tsauri da ya ke jiransu”
Ministan harkokin jiragen saman na Najeriya ya bayyana wannan ne duk a shafinsa na Tuwita. Wannan sanarwa ta zo da kimanin karfe 2:30 na ranar yau Lahadi a agogon Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng