Osinbajo ya bayyana ma Buhari muhimman hanyoyi 2 da zai bi don inganta rayuwar yan Najeriya

Osinbajo ya bayyana ma Buhari muhimman hanyoyi 2 da zai bi don inganta rayuwar yan Najeriya

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya shawarci gwamnatin Najeriya ta bayar da kulawa kyauta ga yan Najeriya marasa lafiya dake asibiti ba tare da biyan sisi ba.

Daily Trust ta ruwaito hakan na cikin shawarwarin da hukumar sayar da kadarorin gwamnati da Osinbajo yake jagoranta ta baiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Coronavirus: Hukumar gwamnatin tarayya ta zaftare kashi 50 na albashin ma’aikatanta

Osinbajo ya shawarci Buhari ya baiwa marasa lafiya kulawa kyauta, kuma ya inganta wutar lantarki a Najeriya, wadannan abubuwa biyu za su matukar amfanar miliyoyin yan Najeriya.

A ranar Talata ne hukumar ta amince da shawarwarin, wanda zasu bayyana su ga shugaban kasa Buhari, tare da kudurin dokar kwaskwarima ga bangaren kiwon lafiya, bada jimawa ba.

Cikin wani sako da kakaakin Osinbajo ya wallafa a shafin Twitter, Laolu Akande, yace daga cikin manyan batutuwan da majalisar ta tattauna akwai batun wuta da kiwon lafiya.

Osinbajo ya bayyana ma Buhari muhimman hanyoyi 2 da zai bi don inganta rayuwar yan Najeriya
Osinbajo tare da yan majalisar hukumar Hoto: Laolu Akande
Asali: Twitter

“Gyaran da gwamnatin Buhari za ta yi zai tabbatar da miliyoyin yan Najeriya da ba su iya biyan kudin asibiti sun samu kyakkyawar kulawa kyauta daga wajen gwamnati da zarar an kaddamar da sabon tsari.” Inji shi.

Mambobin hukumar sun hada da Osinbajo, zababbun ministoci, gwamnan babban bankin Najeriya da kuma shugaban hukumar sayar da kadarorin gwamnatin.

A wani labari kuma, saboda rashin kudaden shiga da hukuma kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya, FAAN, ke fama da shi, ta ce ba za ta ta iya biyan cikakken albashin ma’aikata ba.

Hukumar ta bayyana cewa ma’aikata za su fuskanci canji a albashinsu daga watan Mayu, amma da zarar jirage sun cigaba da tashi za ta cigaba da biyansu cikakkun hakkokinsu.

Hukumar FAAN ta shiga matsalar albashi ne tun bayan da aka dakatar da sauka da tashin jirage a Najeriya a wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus tun a watan Afrilu.

Rashin zirga zirgan jiragen yasa aka samu nakasu a kudaden shigar hukumar, don haka a ranar 19 ga watan Mayu ta sanar da ma’aikatanta halin da ake ciki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel