COVID-19: Buhari zai bayyana matakin dauka na gaba - Shugaban PTF

COVID-19: Buhari zai bayyana matakin dauka na gaba - Shugaban PTF

A yau Litinin ne ake tsammanin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a kan sabbin hanyoyin yakar annobar Coronavirus a kasar nan.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa an yi wa shugaban kasar bayani a gidan gwamnati a kan inda kwamitin yaki da cutar coronavirus ta kasar nan suka tsaya.

Shugaban PTF, wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasar a garin Abuja tare da kungiyarsa.

Shugaban kasar ya nuna gamsuwarsa a kan ci gaban da ake samu a yayin yakar cutar a kasar nan.

Shugaban PTF din ya samu rakiyar ministan lafiya Osagie Ehanire, shugaban NCDC Chikwe Ihekweazu da Dr Sani Aliyu.

Kamar yadda Mustapha ya bayyana, PTF ta soki gwamnatocin jihohin da suka bude wuraren bauta.

COVID-19: Buhari zai bayyana mataki dauka na gaba - Shugaban PTF
COVID-19: Buhari zai bayyana mataki dauka na gaba - Shugaban PTF Hoto: The Cable
Asali: UGC

Ya sanar da manema labarai cewa matakin da shugaba Buhari zai dauka shine bayyana hanyoyi na gaba da za a bi don shawo kan annobar.

SGF yace: "Daga ranar 4 ga watan Mayu zuwa Litinin, kwanaki 13 kenan da saka wasu dokoki. Mu tsammaci sabbin dokoki amma dole sai mun bayyana mishi halin da ake ciki don samun fuskantar gaba.

"A halin yanzu muna kan gaba wajen fuskantar abinda ke damunmu. Ba lamari bane karami a gabanmu kuma dole ne mu yi abinda ya dace.

"Amma idan zamu tuna, a ranar 27 ga watan Afirilu, shugaba Buhari ya yi jawabi ga kasar nan a kan sassauta dokar hana walwala daga 4 ga watan Mayun."

A yayin jawabi a kan martani da kuma yadda 'yan Najeriya ke bin dokokin gwamnatin, Mustapha ya jajanta cewa duk da kashi 99 na jama'ar kasar nan sun san da wanzuwar cutar, da yawa daga ciki ba su kokarin kiyaye dokokin.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Hotunan 'yan ta'adda 20 da dakarun Najeriya suka halaka

Ya jaddada cewa annobar ba za ta tafi da wuri ba don haka alhakin kowa ne yaki da ita.

Ya ce: "COVID-19 ba za ta tafi nan da wata daya ko biyu ba, duk wanda yace za ta tafi yanzu ya yaudari jama'a. Babu riga-kafin cutar a yanzu kuma a kalla sai an dauka watanni 18 ko shekaru biyu kafin a tabbatar da riga-kafin cutar. Hakan na nufin cutar na nan daram.

"Ta yuwu cutar coronavirus ta yadu a mataki zuwa mataki. Za a iya samun sassauci amma ta sake dawowa daga baya. A halin yanzu dole mu koya wa jama'a kiyayewa a matsayin mu na kwamitin yaki da yaduwar ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel