Kannywood: Allah ya yi wa tsohon jarumi, Daudu Galadanci rasuwa

Kannywood: Allah ya yi wa tsohon jarumi, Daudu Galadanci rasuwa

Allah ya yi wa fitaccen tsohon jarumin masana'antar Kannywood, Daudu Galadanci, wanda aka fi sani da Alkalin Kuliya rasuwa.

Tsohon jarumin ya rasu ne a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, da dare.

Za a yi jana'izarsa kamar yadda addinin Islama ya tanada a Galadanci da ke birnin Kano da karfe tara na safiyar Alhamis, 14 ga watan Mayu.

Sakon mutuwar nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jarumin masana'antar, Ali Nuhu, ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Kafin rasuwarsa ana kyautata zaton babu dan was an da ya kai tsufansa ko yawan shekarunsa a harkar fim.

KU KARANTA KUMA: Yadda wata karuwa ta wurgo kwastoma ta tagar otal sanye da kwaroron roba (Bidiyo)

Tun ana wasan dambe da dirama, har aka fara nuna su a talbijin, inda ya rika fitowa a matsayin alkalin shirin ‘Kuliya Manta Sabo’, wanda a nan ne ya samo lakaninsa na Kuliya.

Ya ci gaba da wasanni har zuwa zamanin fina-finan Hausa na Kannywood inda aka dama da shi.

Mutuwarsa na zuwa ne yan makonni bayan mutuwar wani jarumi, Ubale Ibrahim wanda aka fi sani da wanke-wanke.

Mutuwar ta girgiza ‘yan fim ɗin Hausa, musamman da yake ba a ji labarin ko ya yi rashin lafiya ne ba.

Ya rasu ne a safiyar ranar 1 ga watan Mayu, inda aka yi jana’izar jarumin a gidan sa da ke unguwar Rangaza da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo a cikin garin Kano, kuma aka binne shi a makabartar Tudun Murtala.

Dimbin ‘yan fim da sauran jama’a sun halarta.

Cikin manyan ‘yan fim da su ka halarta akwai aminan marigayin, wato Sani Musa Danja, Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, sai kuma Mustapha Nabraska, Abdul Amart, T.Y. Shaban, da Jamilu Ibrahim.

Marigayin, mai kimanin shekaru kusan 50, ya rasu ya bar matar sa ɗaya da ‘ya’ya shida -biyar maza ɗaya mace – da kuma mahaifin sa.

Allah ya gafarta masu, yasa sun huta, ya kyautata tamu idan ta zo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel