Manyan Jam’iyyar PDP su na yunkurin tsige Hassan Hyat a Jihar Kaduna
Jaridar Daily Trust ta fito da rahoto cewa a jihar Kaduna, ana neman hanyar canza shugaban jam’iyyar PDP, Felix Hassan Hyat a dalilin marawa Atiku Abubakar baya a zaben 2019.
Rahoton ya nuna maganar sauke shugaban jam’iyyar adawar ta yi karfi a halin yanzu. Ana zargin Mista Hassan Hyat da goyon bayan Atiku Abubakar a wajen zaben fitar da gwanin PDP.
Atiku ne wanda ya yi nasarar lashe tikitin jam’iyyar PDP na shugaban kasa a bara. Akwai tuhuma kan shugaban PDP na Kaduna na juyawa ‘dan-gida watau Ahmed Makarfi baya a zaben.
Kafin 2015, Kaduna ta na cikin jihohin da PDP ta ke da karfi a arewacin Najeriya har ta kai jihar Kaduna ta fito da mataimakin shugaban kasa Arch. Namadi Sambo daga 2010 har 2015.
A 2015 ne guguwar Muhammadu Buhari ta tarwatsa ginin jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, ta kafa gwamnatin APC. Bayan haka jam’iyyar APC ta samu tulin ‘yan majalisa a gida da tarayya.
KU KARANTA: Abubuwa na neman sake zani a fadar Shugaban kasa bayan mutuwar Kyari
Wasu daga cikin manyan PDP a jihar Kaduna su na ganin zaben 2019 ya yi wa jam’iyyar kyau. Jigon PDP, Abraham Catoh ya ce jam’iyyar ta na tabuka abin kirki a kakashin Hassan Hyat.
Shi ma wani babban jam’iyyar adawar a jihar Kaduna, Danjuma Bello Sarki ya bayyana irin haka. Bello Sarki ya ce Kaduna ce jihar da ta fi kowace ba jam’iyyar PDP kuri’a a babban zaben 2019.
Duk da irin kokarin da PDP ta yi na lashe kujerun majalisar dokoki 10 da na ‘yan majalisar tarayya 6 har da sanata guda a Kaduna a zaben bara, wasu na yunkurin ganin bayan shugaban na ta.
Jaridar ta ce masu harin kujerar shugaban jam’iyya a zaben da za ayi idan abubuwa sun dawo daidai a kasar sun hada da: Hon. Ado Dogo Audu, Hon Bulus Kajang da Hon. Waziri Ashafa.
Felix Hassan Hyat ya musanya zargin yi wa Atiku Abubakar aiki a 2019. Hyat ya ce idan har ‘ya ‘yan jam’iyya sun zabi Atiku a zaben fitar da gwani, ya nuna cewa ya ba ‘ya ‘yan na sa ‘yanci.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng