Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya mutu a Kano

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya mutu a Kano

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Atiku Nagodi, ya mutu ranar Litinin a Kano, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

A cewar SaharaReporters, Nagodi ya mutu ne bayan wata gajeriyar jinya.

Mutuwar Nagodi na daga cikin adadin mutanen da ke cigaba da mutuwa a Kano.

Sai dai, ya zuwa yanzu babu wasu isassun bayanai dangane da mutuwar babban jami'in dan sandan, Kazalika, rundunar 'yan sanda ba ta fitar da jawabi ba.

Nasir Gwarzo, jagoran tawagar ma'aikatan lafiya da aka tura Kano, ya ce su na zargin cewa annobar cutar covid-19 ce sanadiyyar mutuwar mutane a jihar.

Dr. Nasiru Sani Gwarzo ya bayyana cewa cutar COVID-19 ce ta ke kashe mutane a ‘yan kwanakin nan a jihar Kano.

Nasiru Sani Gwarzo ya ce binciken da su ka yi ne ya nuna masu haka.

Kwararren likitan wanda ya na cikin masu yaki da annobar Coronavirus ya shaidawa manema labarai cewa sakamakon gwajin da su ka yi ya nuna COVID-19 ce ke kashe jama’a.

Gwarzo ya yi wannan jawabi a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu, 2020, ya ce sakamakon binciken mace - macen da ake yi a 'yan kwanakin baya bayan nan, ya tabbatar cewa akwai hannun cutar COVID-19.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya mutu a Kano
Mataimakin kwamishinan 'yan sanda; A. M Nagodi
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Dr. Nasiru Gwarzo ya fadi hakan ne yayin da ya ke magana da ‘yan jarida bayan bikin kaddamar da wani dakin gwaji da Alhaji Aliko Dangote ya gina a Kano.

A cewar Dr. Nasiru Gwarzo: “Bari in sanar da ku cewa a mafi yawan mace-macen da aka yi kwanan nan, daga gwajin da aka yi, an gano cewa cutar Coronavirus ce sanadin mutuwar."

DUBA WANNAN: Ma su gudu su gudu: Bidiyon yadda jama'a su ka fece bayan wani mutum ya yanke jiki ya fadi a layin ATM

Ya ce: “Saboda kafin cikakken rahotonmu ya fito nan da mako guda ko kuma ‘yan kwanaki, ya zama dole mutanen jihar Kano su farka daga gyangyadin da su ke yi game da annobar.”

“Ba sabon abu ba ne, kasashen Duniya irinsu Amurka, Sin, Italiya, Sifen, Ingila da Faransa da sauransu, sun yi fama da irin wannan mace-mace mai ban mamaki.” Inji Dr. Gwarzo.

Kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya turo Nasiru Sani Gwarzo da tawagarsa su zo jihar Kano domin su binciki abin da ya ke jawo mutuwar Bayin Allah bini-bini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel