An cafke Talatu Idris; mai jinyar covid-19 da ta tsere daga cibiyar killacewa a Taraba

An cafke Talatu Idris; mai jinyar covid-19 da ta tsere daga cibiyar killacewa a Taraba

Gwamnatin jihar Taraba ta ce ta damke wata majinyaciya da ta tsere daga cibiyar killacewa ta jihar bayan an tabbatar tana dauke da cutar coronavirus.

Wacce aka damke din mai suna Talatu Idris an kama ta ne tare da mayar da ita cibiyar killacewa.

Kwamishinan lafiya na jihar kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar, Dr Innocent Vakkai ya bayyana hakan a Jalingo, babban birnin jihar a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa an fara zakulo wadanda suka yi ma'amala da masu cutar a jihar don hana yaduwarta.

An cafke Talatu Idris; mai jinyar covid-19 da ta tsere daga cibiyar killacewa a Taraba
An cafke Talatu Idris; mai jinyar covid-19 da ta tsere daga cibiyar killacewa a Taraba
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, kwamishinan yace za a kara yi wa majinyatan cutar na jihar wani gwajin don sanin halin da suke ciki.

Ya kara da musanta rade-radin cewa an bude makarantu da wuraren bauta na jihar.

Kamar yadda yace, "Makarantun mu da wuraren bauta za su ci gaba da zama a rufe. Ana shawartar jama'a da su ci gaba da kiyaye dokokin hana yaduwar cutar a kwanaki biyun da ake barin zirga-zirga a jihar."

Ya kara da cewa jihar ba za ta ba almajiran da aka kawo daga wata jihar masauki ba har sai an tabbatar da cewa basu dauke da muguwar cutar.

KU KARANTA KUMA: Tsohon hadimin marigayi Yar'adua ya mutu a Kano

A halin yanzu, jihar Taraba na da mutum 8 da ke dauke da cutar coronavirus kuma ta wajabta saka takunkumin fuska na kwanaki biyun da take barin walwalar jama'a a jihar.

A gefe guda, gwamnatin Katsina ta bayar da umarnin sake rufe wasu manyan kasuwanni uku da ke ci sati - sati a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi, 03 ga watan Mayu.

Kasuwanni da wannan umarni ya shafa sune; Garkin Daura, Dusti, da Kayawa.

An rufe kasuwannin ne bayan gwamnati da ma su ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu a kan hauhawar mutanen da ke kamuwa da cutar covid-19 a jihar Katsina.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng