Covid-19: An rufe fadar sarkin Daura bayan mutuwar matar sarki

Covid-19: An rufe fadar sarkin Daura bayan mutuwar matar sarki

- An rufe fadar masarautar Daura a jihar Katsina saboda fargabar bullar annobar cutar covid-19

- Karamar hukumar Daura gwamnatin jihar Katsina ta fara rufewa bayan mutuwar wani mai dauke da kwayar cutar covid-19

- A ranar 17 ga watan Afrilu, matar sarkin Daura ta mutu ta na da shekaru 70 a duniya

Kimanin sati biyu da suka gabata, gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe karamar hukumar Daura biyo bayan mutuwar wani mai dauke da kwayar cutar covid-19.

A wani labari da jaridar Daily Trust ta wallafa a yau, Litinin, 04 ga watan Mayu, ta bayyana cewa an rufe fadar masarautar Daura bayan samun bullar annobar covid-19.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, dan asalin karamar hukumar Daura ne.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa, ya tabbatar da rufe fadar sarkin tare da bayyana cewa sakamakon gwajin da ake jira ne kadai zai nuna lokacin da za a bude fadar.

"Ba wani sabon abu bane, haka tsarin ya ke duk duniya, matukar an samu mai dauke da kwayar cutar covid-19. An rufe fadar yayin da aka dauki jinin mutane zuwa cibiyar gwaji," a cewarsa.

Da ya ke magana a kan lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ce, "mu dama a wurin rundunar 'yan sanda, karamar hukumar Daura a rufe ta ke, hakan kuma ya shafi kowanne lungu da sako da kuma kowanne gida.

Covid-19: An rufe fadar sarkin Daura bayan mutuwar matar sarki

Fadar masarautar Daura Hoto: Daily Trust
Source: UGC

"Aikin rundunar 'yan sanda shine tabbatar da dokar gwamnati a kan dukkan jama'a."

A ranar 17 ga watan Afrilu ne uwargidan sarkin Daura, Hajiya Binta Umar, ta mutu bayan ta sha fama da wata doguwar jinya. Ta mutu ta na da shekaru 70 a duniya.

DUBA WANNAN: Covid-19: Sakamakon gwajin hadiman Buhari da su ka halarci jana'izar Abba Kyari ya fito

An tabbatar da samun karin mutane 8 da su ka kamu da kwayar cutar covid-19 a ranar Lahadi, kamar yadda cibiyar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar.

Yanzu haka akwai jimillar mutane 46 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar Katsina.

A yayin da aka sallami mutane 6 da su ka warke daga cutar covid-19 a Katsina, cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 7.

Daga cikin wadanda su ka mutu akwai wani likita mazaunin garin Daura mai suna Dakta Aliyu Yakubu, wanda ya mutu a cikin satin da ya dawo daga jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel