Mai jinyar covid-19 da ya gudu daga cibiyar killacewa ya mutu a gida a Kebbi
- An yi gudu babu tsira yayin da mai dauke da kwayar cutar covid-19 ya mutu a gida bayan ya yi gudun cibiyar killacewa a jihar Kebbi
- Marigayin wani dattijo ne mai shekaru 60 da ke fama da ciwon sukari da hawan jini
- Kwamishinan lafiya a Kebbi, Alhaji Jaafaru Mohammed, ya sanar da hakan yayin da ya ke bayar da jawabi a kan bullar annobar covid-19 a jihar
Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da mutuwar wani mai jinyar covid-19 wanda ya gudu daga cibiyar killacewa bayan an dauki jininsa domin gudanar da gwajin kwayar cutar.
Marigayin wani mutum ne mai shekaru 60 da ke fama da ciwon sukari da hawan jini.
Yahaya Sarki, kakakin gwamnan jihar Kebbi, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya aikawa manema labarai a ranar Asabar.
Sarki ya bayyana cewa kwamishinan lafiya a Kebbi, Alhaji Jaafaru Mohammed, ya sanar da hakan yayin da ya ke bayar da jawabi a kan bullar annobar covid-19 a jihar
Yayin da ya ke gabatar da jawabin, kwamishinan ya ce, "mutum na biyu da annobar covid-19 ta hallaka a jihar Kebbi, wani mutum ne mai shekaru 60 da aka san shi da ciwon sukari da hawan jini a asibitin tarayya da ke Birnin Kebbi.
"Danginsa sun kawo shi cibiyar daga asibitin koyarwa na jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto.
"Likitan da ke duba shi ya yi zargin cewa ya kamu da kwayar cutar, a saboda haka sai ya tuntubi kwamitin kar ta kwana na jiha a kan annobar covid-19," a cewar Kwamishinan.
Sannan ya cigaba da cewa, mutumin ya gudu don a kar a kai shi cibiyar killacewa bayan an dauki jininsa zuwa dakin gwaji a ranar 25 ga watan Afrilu.
Ya ce mutumin ya mutu washegari, ranar 26 ga watan Afrilu, a gida.
DUBA WANNAN: Covid-19: Ku fidda ran daidaituwar al'amura a cikin shekarar nan - Shugaban NCDC
"An dauki gawarsa zuwa dakin ajiye gawa na asibitin UDUTH, sabanin labarin da wasu ke yadawa a kan cewa an tafi da gawarsa zuwa jihar Benuwe domin binnewa.
"Sakamakon gwajinsa da ya fito a ranar 29 ga watan Afrilu ya nuna cewa ya na dauke da kwayar cutar, lamarin da yasa kwamiti ya shiga neman wadanda ya yi mu'amala da su kafin fitowar sakamakonsa," kamar yadda kwamishinan ya bayyana.
A cewar kwamishinan, sun gano wasu mutane 12 da ke da kusanci da marigayin tare da wasu sauran mutane 17 da ya yi mu'amala da su.
Ya sanar da cewa an dauki jinin dukkan mutane tare da turawa zuwa dakin gwaji da ke UDUTH a jihar Sokoto.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng