An kama wasu Katsinawa uku da su ka zazzagi Buhari a dandalin sada zumunta

An kama wasu Katsinawa uku da su ka zazzagi Buhari a dandalin sada zumunta

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta sanar da kama wasu mutane uku da su ka zagi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

An kama mutanen ne bayan wani faifan bidiyonsu da su ke zagin shugabannin ya kewaya a dandalin sada zumunta.

Mutanen uku da aka kama sun hada da wani dattijo dan shekara 70 mai suna Lawal Abdullahi Izala, da Bahhajje Abu, da Hamza Abubakar, dukkansu mazauna unguwar Gafai a cikin garin Katsina.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce an karar da rundunar 'yan sanda a kan wani faifan bidiyo da wani Lawal Abdullahi, wanda aka fi sani da 'Izala', ya ke zagin Buhari da Masari a cikinsa.

"A Saboda haka, kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina, CP Sanusi Buba, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, wanda ya kai ga an kama mutanen uku," a cewarsa.

An kama wasu Katsinawa uku da su ka zazzagi Buhari a dandalin sada zumunta
Buhari da Masari
Asali: UGC

Ya kara da cewa, "a yayin da mu ke tuhumarsu, wadanda ake zargi sun amsa laifinsu.

"Ya kamata jama'a su sani cewa rundunar 'yan sanda ba za ta nade hannayenta tana kallon wasu tsirarun marasa tarbiyya suna sabawa dokokin kasa ba.

DUBA WANNAN: Ministocin Buhari sun bullo da sabuwar tsirfa a kan nada madadin marigayi Abba Kyari

"Duk wanda aka samu ya na amfani da dandalin sada zumunta domin zagin wani mutum ko wasu mutane, zai fuskanci fushin doka, kamar yadda aka tanada a karkashin dokokin hukunce - hukuncen manyan laifuka a yanar gizo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel