Yanzu-yanzu: Trump ya kira Buhari, ya yi alkawarin aiko da tallafi

Yanzu-yanzu: Trump ya kira Buhari, ya yi alkawarin aiko da tallafi

- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kira shugaba Muhammadu Buhari a wayar tafi-da-gidanka a yau Talata

- Kamar yadda ministan yada labarai, Lai Mohammed ya bayyana, Trump ya kira ne don jajantawa Buhari halin annobar da kasar nan ta shiga

- Shugaban kasar Amurkan ya bayyana cewa zai aiko da na'urorin taimakon numfashi don amfanin asibitocin kasar nan

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari a waya a ranar Talata.

Ya kira ne don jajantawa Najeriya halin da ta shiga na mummunar annobar Covid-19, jaridar The Cable ta wallafa.

Kamar yadda Lai Mohammed, ministan yada labarai ya bayyana, shugaba Trump din ya dauka alkawarin aike wa Najeriya da sakon na'urorin taimakon numfashi.

Mohammed ya sanar da hakan ne a yayin jawabin kwamitin shugaban kasa na yakar annobar Covid-19.

Kamar yadda Turmp ya yi alkawari, zai aiko da na'urorin taimakon numfashin ne don amfanin asibitocin Najeriya.

Yanzu-yanzu: Trump ya kira Buhari, ya yi alkawarin aiko da tallafi
Yanzu-yanzu: Trump ya kira Buhari, ya yi alkawarin aiko da tallafi
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: NAFDAC ta tabbatar da ingancin shinkafar da muka rabawa jihohi - FG

Karin bayani na nan tafe...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel