Majalisar dokokin tarayya ta dawo zama bayan hutun COVID-19

Majalisar dokokin tarayya ta dawo zama bayan hutun COVID-19

Mambobin majalisar dokokin tarayya sun dawo zaman majalisa bayan kimanin makonni biyar da tafiya hutu a kan annobar coronavirus.

Yan majalisa na dattawa da na wakilai sun koma zauren majalisar a Abuja, a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, bayan sun tafi hutu duk a cikin matakan hana yaduwar cutar COVID-19 a kasar.

A majalisar dattawa, shugaban majalisar, Ahmad Lawan, ya jagoranci mambobinta zuwa zauren, inda aka fara tattaunawa da misalin karfe 10:30 na safe, jim kadan bayan sun samu waje sun zazzauna.

Majalisar dokokin tarayya ta dawo zama bayan hutun COVID-19

Majalisar dokokin tarayya ta dawo zama bayan hutun COVID-19
Source: UGC

A yayinda ake tsaka da samun hauhawan masu COVID-19 a kasar, an bukaci sanatocin su bayar da tazara a tsakaninsu ta hanyar tsallake kujeru bibbiyu wajen zamansu.

Jim kadan da fara zaman, sai yan majalisar dattawan suka shiga ganawar sirri.

Hakazalika, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya jagoranci yan majalisar wakilai cikin zauren majalisa domin zantawa.

KU KARANTA KUMA: Diyar Abba Kyari ta fada ma magauta su rabu da babanta ya kwanta cikin aminci

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar waikilai ta tsayar da ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, 2020, a matsayin ranar da zata dawo daga hutun da ta tafi.

Jaridar 'OderPaperNG' ta rawaito cewa ta ga sakonnin sanarwa da aka aikewa mambobin majalisar da yammacin ranar Lahadi.

A cikin sakon sanarwar, mai dauke da sa hannun Patrick A. Giwa, magatakardar majalisa, an shawarci sauran hadiman mambobin majalisa su cigaba da zama a gida zuwa sanarwa ta gaba.

A cewar sanarwar, "za a yi zaman majalisar ne bisa biyayya ga shawarwarin hukumar NCDC da kuma wasu sabbin matakai da majalisa ta dauka."

Sanarwar ta bayyana cewa; "mu na sanar da dukkan mambobin majalisar wakilai cewa za a dawo zaman majalisa a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, da misalin karfe 10:00 na safe.

"Ana shawartar mambobi a kan su kiyaye da sabon lokacin da aka bayyana a matsayin ranar dawowa daga hutun.

"Za a gudanar da zaman majalisa bisa kiyaye matakan da hukumar NCDC ta shimfida da kuma wasu karin matakai da majalisa ta dauka, wanda za a aika wa kowanne mamba."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel