Azumin bana: An shirya wurin da Sheikh Ahmed Gumi zai gudanar da Tafsiri

Azumin bana: An shirya wurin da Sheikh Ahmed Gumi zai gudanar da Tafsiri

Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi, ya bayyana cewa tuni ya kammala shirin fara Tasirin Al-Qur’ani mai girma, na azumin bana da ake shirin farawa.

Shehin malamin ya cezai gudanar da Tafsirin nasa ne a gidansa wanda ke jahar Kaduna. Ya kuma bayyana cewa mutane 10 ne kadai za su samu halartan tafsirin.

Sai dai kuma, Gumi ya ce za a nadi sauti da bidiyo na karatun nasa inda daga baya za a watsa a kafafen sada zumunta.

Hakan na da nasaba ne da kokarin da ake yin a hana yaduwar annobar COVID-19 wacce ake fama da ita a fadin kasar.

Ga hotunan wurin tafsirin a kasa:

Azumin bana: Wurin da Sheikh Ahmed Gumi zai gudanar da Tafsiri (hotuna)
Azumin bana: Wurin da Sheikh Ahmed Gumi zai gudanar da Tafsiri
Asali: Twitter

Azumin bana: Wurin da Sheikh Ahmed Gumi zai gudanar da Tafsiri (hotuna)
Azumin bana: Wurin da Sheikh Ahmed Gumi zai gudanar da Tafsiri (hotuna)
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Gwamnatin Kano ta musanta jita jitan mutuwar mutane birjik a Kano

A baya mun ji cewa kwamitin Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna ta yanke shawarar dakatar da gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma kamar yadda aka saba yi a cikin Masallacin.

Sheikh Ahmad Gumi ne yake gudanar da tafsiri a Masallacin a duk lokacin azumin watan Ramadana, amma an samu sauyi a azumin bana saboda COVID-19.

Babban limamin Masallacin, Farfesa Muhammad Sulaiman Adam ne ya bayyana haka, inda yace a bana Malam Ahmad Gumi zai gudanar da tafsirin ne daga wani wuri na daban.

Sulaiman yace Malam Gumi ne kadai zai gudanar da Tafsirin tare da majabakinsa, kuma za’a watsa karatun a kafafen sadarwa na gani da na saurare, da shafukan sadarwar zamani.

Haka zalika, Sheikh Sulaiman ya kara da cewa Masallacin Sultan Bello zai cigaba da zama a garkame har sai lokacin da gwamnati ta bayar da izinin bude Masallatai.

Daga karshe Shehin Malamin ya bayyana dalilin daukan wannan mataki shi ne don dakile yaduwar cutar, don haka ya nemi Musulmai su cigaba da addu’a domin Allah Ya yaye masifar.

Shi ma Sheikh Gumi ya tabbatar da bayanin Sheikh Sulaiman, inda yace zai gudanar da tafisirin bana ne a wani wuri da ya dace da ka’idojin da hukuma ta shimfida da na masu kiwon lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng