Ohaenaze ta na so Ibo ya dare kujerar COS da Malam Kyari ya mutu ya bari

Ohaenaze ta na so Ibo ya dare kujerar COS da Malam Kyari ya mutu ya bari

A karshen makon da ya gabata ne COVID-19 ta kashe shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya. Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Youth Council ta yi magana bayan cikawarsa.

Kungiyar ta OYC ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara la’akarin zaben mutumin Ibo a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadarsa bayan rasuwar Abba Kyari.

Wannan kungiya ta Matasan masu kare hakkin mutanen Ibo a Najeriya ta bayyana cewa an yi babban rashi a game da rasuwar hadimin shugaban kasar wanda ya cika a ranar Juma’a.

Ohanaeze Ndigbo Youth Council ta fitar da jawabi ne a ranar Lahadi 19 ga watan Afrilu, 2020.

A wannan jawabi, kungiyar ta yi wa Kyari addu’ar Ubangiji ya yafe masa duk kura-kuransa.

Okechukwu Isiguzoro wanda shi ne shugaban OYC ya fitar da wannan jawabi tare da Sakatarensa na kasa watau Okwu Nnabuike.

Bayan gabatar da ta’aziyya da addu’o’i ga mamacin, kungiyar ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna halin girma, ya tabbatarwa Duniya cewa lallai shi Uban kowa ne a Najeriya.

KU KARANTA: Kwamishinan da ya rasa kujera saboda rasuwar Kyari ya yi magana

Ohaenaze ta na so Ibo ya dare kujerar COS da Malam Kyari ya mutu ya bari
Cutar Coronavirus ta kashe Malam Abba Kyari a ranar Juma’a
Asali: Depositphotos

Mista Okechukwu Isiguzoro da Nnabuike su ka ce shugaban kasar zai canzawa mutane ra’ayinsu a kan shi ne ta hanyar zakulo wanda zai maye wannan gurbi mai tsoka daga Yankin Kudu.

Wannan kungiya ta bukaci sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya fito daga cikin magoya bayansa na mutanen Ibo da ke Kudu maso Gabashin kasar ko bangaren Neja-Delta.

OYC ta ce akwai wadanda su ke tare da shugaban kasar tun lokacin da ya shiga siyasa a 2003 zuwa yau.

Kungiyar ta ce Buhari ya na ma iya dauko hadiminsa har daga cikin ‘yan adawa.

“Wannan ce babbar damar da shugaba Buhari ya ke da ita na warkar da Najeriya daga cutar wargajewa da tarwatsewa. Kai, Ibo ne ya shirya yadda jam’iyyu su ka narke a tafiyar APC.”

A ganin matasan na Ohanaeze, idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemo hadiminsa daga yankin Ibo, to ya nuna bajintarsa a siyasa, kuma zai goge kallon da wasu ke yi masa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel