Najeriya ce ta kasance farko a gaban Malam Abba Kyari – Ibrahim Babangida

Najeriya ce ta kasance farko a gaban Malam Abba Kyari – Ibrahim Babangida

Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ya shiga cikin sahun wadanda su ka yi magana game da rasuwar babban hadimin shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari.

Jaridar Tribune ta rahoto Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya na yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ta’aziyyar rashin da ya yi na shugaban ma’aikatan fadarsa.

Ibrahim Babangida ya fitar da jawabi ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilun 2020.

Malam Abba Kyari ya rasu ne a ranar Juma’a bayan ya yi fama da cutar COVID-19 na makonni.

Babangida ya bayyana Marigayin a matsayin mutum mai kishi, da tsantseni da dabara. Tsohon shugaban ya kuma bayyana Abba Kyari da wanda ya cancanci mukamin da ya rike.

A cewarsa, Abba Kyari ya bautawa kasarsa Najeriya da gaske, kuma ya nunawa shugaba Buhari amana a matsayin abokinsa kuma mai ba shi shawara na tsawon shekara da shekaru.

“Kyari ya kasance a ko yaushe shirye ya ke da ya ba ka taimakon da ka ke bukata wajen dabbaka tsare-tsare da manufofin gwamnatinka.” Janar din ya ce shugaban kasar ya yi rashi.

KU KARANTA: Gwamnoni sun aikawa Buhari takarda bayan COVID-19 ta kashe Kyari

Najeriya ce ta kasance farko a gaban Malam Abba Kyari – Ibrahim Babangida

Babangida ya yi wa Shugaba Buhari da Iyalin Kyari ta'aziyya
Source: Twitter

“Ba ni da shakka ko kadan game da cewa Kyari ya yi duk ayyukan da aka daura masa kamar yadda ya dace, ganin yadda ya san aiki kuma ya cancanta, ya kasance mai gaskiya.”

Babangida ya kuma bayyana Marigayin a matsayin mutum maras girman kai. “A kullum ya kan sa mutanen kasar nan farko, sannan Najeriya sai kuma karon kanka a bakin aikinsa.”

“Babu tababa, kai da Iyalinsa za su ku fi kowa jin rashin Abba Kyari, a matsayinmu na Musulmai mun yarda cewa za mu komawa Mahallicinmu, Allah Madaukaki mai iko kan rayuka.”

“An rahoto a wani hadisin Manzo Annabi Muhammad SAW cewa duk wanda annoba ta kashe, ya mutu shahidi, ina addu’ar ace Kyari ya dace da falala da martabar shahada.” Inji sa.

Tsohon shugaban kasar ya ce Buhari ya rasa aboki, abin kauna, amini, wanda ya yi wa kasa aiki tare da hakuri da kishi na Malam Abba Kyari, wanda ya mutu a rana mai daraja ta Juma’a.

A karshe Babangida ya yi kira ga Buhari a matsayinsa na jajirtaccen Musulmi mai imani kuma tsohon Soja, ya dage wajen ganin an yi maganin wannan annoba ta COVID-19 a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel