Yanzu Yanzu: Karin mutane biyar sun kamu da coronavirus a Kano

Yanzu Yanzu: Karin mutane biyar sun kamu da coronavirus a Kano

- Ma'aikatar lafiya ta jahar Kano ta bayyana cewa an sake samun karin mutane biyar da suka kamu da cutar coronavirus a jahar

- Ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu

- A yanzu jimlar mutane tara kenan suka kamu da annobar ta COVID-19 a jahar

Ma’aikatar lafiya ta jahar Kano ce ta bayyana hakan a shafin twitter a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu.

A sakon da ya wallafa a shafinta nata, ta ce ya zuwa karfe 10:25 na safiyar Laraba, adadin masu dauke da cutar a Kano ya kai tara.

A baya mun ji cewa mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe jihar na mako daya.

Dokar hana shige da fice a jihar Kano din za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2020.

Kamar yadda mai bada shawara ta musamman ga gwamnan ya wallafa, ana sa ran dokar hana shige da ficen za ta yi aiki ne mako daya cif kafin a ga abinda hali yayi.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta sallami mutum 1 da ya warke

A tsawon lokacin, ba a bukatar kaiwa da kawowar jama'a ko ababen hawa a jihar. Gwamnan ya tabbatar da cewa jami'an tsaro za su damke duk wanda aka kama da laifin take dokar.

Wannan dokar ta biyo bayan samun mutane hudu masu dauke da cutar coronavirus da aka yi a jahar Kano.

A wani labari na daban, Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje ta ce za ta rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jihar tare da tsananta dokar hana shiga da fice a kan iyakokinta.

Hakan kuwa ya faru ne sakamakon bullar muguwar cutar coronavirus a jihar a ranar Asabar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa BBC cewa tuni aka killace wanda aka samu da cutar a asibitin Pfizer na kwanar Dawaki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel