Coronavirus ta sake kashe wani mutum a Lagas

Coronavirus ta sake kashe wani mutum a Lagas

- Cutar coronavirus ta sake kashe wani mutum a jahar Lagas

- Kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a shafin Twitter

- Ya ce a yanzu jimlar mutane biyar kenan suka mutu a jahar sakamakon COVID-19

Gwamnatin jahar Lagas a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, ta tabbatar da mutuwar wani mara lafiya sakamakon cutar coronavirus a jahar.

Kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi, wanda ya bayyana hakan a shafin Twitter, ya ce a yanzu mutane biyar kenan suka mutu a jahar.

Ya ce mutumin ya rasu ne sakamakon tabarbarewar lafiya da ke da nasaba da coronavirus.

Abayomi ya kara da cewa an samu sabbin mutane 11 da suka kamu a ranar Asabar. A yanzu jahar na da jimlar mutane 177 da suka kamu da COVID-19.

Kwamishinan ya ce jahar ta sallami mutane 50 da suka warke.

Coronavirus ta sake kashe wani mutum a Lagas
Coronavirus ta sake kashe wani mutum a Lagas
Asali: UGC

“An samu sabbin mutane 11 da suka kamu da COVID-19 a Lagas a ranar 11 ga watan Afrilu, 2020. Gaba daya wadanda suka kamu a jahar Lagas sun kama 177.

“Labari mai dadi shine cewa an sallami sabbin mutane hudu da suka warke.

“A yanzu haka an sallami jimlar mutane 50. Abun bakin ciki, an sake samun wanda ya mutu a Lagas inda suka zama mutane biyar.

“Don haka muna bukatar mutane da su yi gwajin COVID-19 da wuri sannan a fara kula da mutum kan lokaci domin tsirar da rayuka.

“A kira layin neman agaji na COVID-19 08000CORONA; domin kai rahoton duk wani lamari da ke da alaka da COVID-19,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Hukumar LASUTH ta killace Ungonzoman da su ka kula da Mai cutar COVID-19

A wani labarin kuma, mun ji cewa an samu tashin hankali a jihar Anambara yayinda aka nemi mutumin farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar aka rasa.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar ranar Juma'a cewa an tabbatar da bullar cutar ta COVID-19 a jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel