Yanzu Yanzu: Shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jahar Kano ya yi murabus

Yanzu Yanzu: Shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jahar Kano ya yi murabus

- Shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jahar Kano ya yi murabus

- Abdulqadir Dambo ya ce murabus din nasa ya fara aiki daga ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu

- Hakan na kunshe ne a wata wasika da ya aike wa babban sakataren gwamnatin jahar

Shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jahar Kano, Alhaji Sani Abdulqadir Dambo ya yi murabus daga kujerarsa.

A cikin wata wasika da ya aike zuwa ga sakataren gwamnatin jahar, Abdulqadir Damboa, ya ce murabus din nasa ya fara aiki daga ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jahar Kano ya yi murabus
Yanzu Yanzu: Shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jahar Kano ya yi murabus
Asali: Twitter

Sai dai babu wani cikakken bayani kan dalilin murabus din nasa a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A gefe guda kuma, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta karawa ma'aikatanta hutun zama a gida na tsason wasu sati biyun domin dakile yaduwar cutar covid-19 a jihar.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano, ne ya sanar da hakan yayin da ya karbi rahoton kwamitin wucin gadi da ya kafa domin neman tallafin kudi.

Ya ce karin wa'adin hutun yana daga cikin shawarar da gwamnatinsa ta yanke a matsayin rigakafin kare jama'a daga kamuwa da cutar covid-19 a jihar.

"Akwai fargaba har yanzu, saboda har yanzu yawan masu kamuwa da kwayar cutar da wadanda cutar ta kashe karuwa yake yi a Najeriya," a cewar Ganduje.

Bayan karbar rahoton kwamitin, gwamna Ganduje ya jinjinawa mambobin kwamitin tare da yabawa aikin da suke yi. Kazalika, ya basu tabbacin cewa nan bada dadewa ba za a raba tallafin da aka samu ga mabukata.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin kuma shugaban jami'ar Bayero ta Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya sanar da gwamnan cewa yanzu haka akwai tsabar kudi miliyan N364.6 a asusun banki.

Sauran kayan tallafi da jama'a suka bayar ta hannun kwamitin sun hada da kayan abinci da sauran kayan amfani a gida.

Daga cikin wadanda suka bayar da tallafi mafi tsoka akwai kungiyar 'yan kasar Lebanon mazauna Kano, wadanda suka bayar da tallafin kayan abinci da darajar kudinsu ya wuce miliyan N100m.

Bayan kammala taro da mambobin kwamitin, gwamna Ganduje ya kai ziyara cibiyar killace masu dauke da cutar covid-19 da gidauniyar Dangote tare da hadin gwuiwar gwamnatin jihar Kano suka samar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel