NSIP: Hadimar Buhari ta mayarwa da Lawan da Gbajabiamila martani a kan sukar shirin bayar da tallafi

NSIP: Hadimar Buhari ta mayarwa da Lawan da Gbajabiamila martani a kan sukar shirin bayar da tallafi

Hadimar Buhari ta mayarwa da shugabannin majalisun tarayya martani a kan sukar kaddamar da shirin bayar da tallafi ga 'yan kasa (NSIP).

Maryam Uwais, mai bawa shugaban kasa shawara a kan shirin NSIP, ce ta mayarwa da shugabannin majalisar martani a cikin wani jawabi da ta fitar ranar Laraba.

Shirin NSIP ya kunshi tsarin ciyar da daliban makarantun firamare, tsarin samar da aiki ga matasan da suka kammala manyan makarantu (N-Power), bayar da tallafin kudi ga dattijai da hajiyayyu da kuma tsarin bayar da rancen kudi ga kananan masu sana'o'i.

Maryam ta bayyana wasu daga cikin ikirarin 'yan majalisar a matsayin karya, wasu 'abin takaici' da kuma wasu masu 'hatsari'.

Shugabannin majalisa, Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila su na ganin gwamnatin tarayya ta gaza sosai wajen dabbaka tsare-tsaren NSIP da aka kirkiro domin inganta rayuwar Talaka.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe fiye da Naira Tiriliyan biyu a wannan tsari na NSIP daga 2016 zuwa yanzu.

NSIP: Hadimar Buhari ta mayarwa da Lawan da Gbajabiamila martani a kan sukar shirin bayar da tallafi
Sadiya Farouq da Maryam Uwais
Asali: Facebook

Amma shugabannin majalisar su na ganin har yanzu ba a kai ga cimma muradun shirin ba.

Shugabannin majalisar sun yi wannan bayani ne a Ranar Talata a lokacin da su ka gana da Ministar bada agaji da tallafin gaggawa, Hajia Sadiya Umar Farouq.

DUBA WANNAN: Za a sha wuta kyauta na tsawon wata 2 a Najeriya, FG da Discos sun amince

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan da Rt. Hon. Femi Gbajabiamila sun koka a kan cewa kudin da aka warewa wannan tsari ba su kai ga ainihin wadanda aka tanadi tsarin domin su ba a Najeriya.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa a dalilin haka ne Dr. Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila su ka bukaci Ministar ta sake duba tafiyar wadannan shiri domin ganin wadanda aka tsara abin dominsu su na mora.

Ahmad Lawan ya ke cewa Majalisar tarayya ta damu da wannan shiri da aka kirkira domin rage radadin Marasa karfi, don haka ne ya bukaci a tabbatar wajen ganin Talakawa sun amfana.

Sanatan ya bukaci sabuwar ma’aikatar da ke da alhakin kula da wannan shiri ta yi kokari wajen ganin an waiwayi wadanda talauci ya yi wa kullin goro a wannan lokaci na annobar COVID-19.

“Ina fada maku cewa mafi yawan wadanda za su amfana da wannan tsari ba su da wutar lantarki, ba su san shafin yanar gizo ba. Ba su da asusu a banki, don haka ba su da lambar BVN,” a cewarsa.

Femi Gbajabiamila ya tambayi Ministar: “Ina ku ka samu sunayen Talakawanku, ta ya ku ka yi kason, wanne sharadi aka zaba, wanne yanki ku ka dauko,” ya ce akwai bukatar a samu amsoshin wadannan tambayoyi.

Shugaban majalisar wakilan ya bayyana cewa a matsayinsu na Wakilan jama’a dole su san yadda wannan tsari ya ke aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel