Rundunar soji ta yaye wasu dakarunta da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman (Hotuna)

Rundunar soji ta yaye wasu dakarunta da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman (Hotuna)

A kokarinta na cigaba da yakar aiyukan ta'addanci da 'yan ta'adda a fadin kasa, rundunar sojojin Najeriya ta yaye wasu dakarunta da aka bawa horo a kan sabon salon yaki na musamman.

Dakarun sojin da aka bawa horon na musamman a kan yadda ake sarrafa bindiga daga bakin kofar jirgi mai saukar ungulu (HBDG), sun hada da dakarun rundunar sojin sama (NAF) 19 da kuma sojojin kasa (NA) 12.

An zaba sojojin daga runduna daban-daban ne domin hada karfi da kara bayar da horo bai daya ga dakarun sojin da ke atisayen yaki da ta'addanci.

An gudanar da bikin yaye dakarun sojojin ne a yau, Litinin, 6 ga watan Afrilu, a wata cibiyar bayar da horo ta NAF (RTC) da ke Kaduna.

A zamnsu na tsawon sati biyar a RTC, an bawa dakarun sojin horo a kan salo da dabaru na musamman a kan bayar da taimako daga sararin samaniya ga dakarun soji da ke yaki da 'yan ta'adda a kasa.

A cikin watan Yuni na shekarar 2019 ne rundunar 'yan sanda ta bawa jami'anta irin wannan horo na BDG.

DUBA WANNAN: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

Da yake gabatar da jawabi a wurin bikin yaye dakarun sojin, shugaban rundunar NAF (CAS), Air Marshal Sadique Abubakar, wanda shugaban sashen bayar da horo na NAF, Air Vice Marshal (AVM) James Gwani, ya wakilta, ya bayyana cewa bawa dakarun soji irin wannan horo ya zama wajibi idan aka yi la'akari da irin nau'i da salon aiyukan ta'addanci da kasa ke fama da su.

Ya bayyana cewa samun wadannan dabaru da sojojin suka yi zai taimaka matuka wajen bayar da taimako ga sauran sojoji a yayinda suke fafatawa da 'yan ta'adda a kasa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Air Commodore Ibikunle Daramola, darektan hulda da jama'a da yada labaran rundunar NAF, ya wallafa a shafukan sada zumunta na rundunar a ranar Litinin.

Rundunar soji ta yaye wasu dakarunta da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman (Hotuna)

Dakarun da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman
Source: Twitter

Rundunar soji ta yaye wasu dakarunta da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman (Hotuna)

Dakarun soji da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman
Source: Twitter

Rundunar soji ta yaye wasu dakarunta da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman (Hotuna)

Dakarun da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman
Source: Twitter

Rundunar soji ta yaye wasu dakarunta da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman (Hotuna)

Rundunar soji ta yaye dakarunta da aka bawa horo a kan salon yaki na musamman
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel