NMA da TUC ba su yi na’am da aikowa Najeriya Malaman lafiyan China ba

NMA da TUC ba su yi na’am da aikowa Najeriya Malaman lafiyan China ba

Kungiyar NMA ta Likitocin Najeriya da kuma TUC ta ‘Yan kasuwa sun nuna rashin amincewar su da gayyatar da gwamnatin tarayya ta yi wa Likitoci da Ungonzoma daga kasar Sin.

Wadannan kungiyoyi sun nuna cewa sam ba su tare da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wannan mataki da ta dauka na yaki da cutar Coronavirus da ta addabi kasashe.

A Ranar Juma’ar da ta gabata ne Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya shaidawa Najeriya cewa wasu Malaman kiwon lafiya daga kasar Sin za so Najeriya domin taimakawa asibitocinmu.

Bayan haka, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa za a aikowa Najeriya kayan aikin asibiti wanda daga cikin har da na’urar taimakawa numfashi, wannan duk don a yaki cutar COVID-19.

Sai dai shugaban kungiyar Likitoci a Najeriya, Dr. Francis Faduyile, a wani jawabi da ya fitar wanda ya shiga hannun Daily Trust, ya nemi gwamnati ta dakatar da wannan magana.

KU KARANTA: Gwamnatin Sokoto za ta rika bibiyar Baki wajen yaki da cutar COVID-19

NMA da TUC ba su yi na’am da aikowa Najeriya Malaman lafiyan China ba
Shugaban Najeriya Buhari tare da shugabannin kungiyar NMA kwanaki
Asali: UGC

Francis Faduyile a madadin NMA ya fito Ranar Lahadi ya na kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki ne na musamman na gyara sha’anin kiwon lafiya, ba tare da wani bata lokaci ba.

NMA ta koka da yadda gwamnatin Buhari ta yi watsi da ita wajen daukar matakan da ya kamata a bi wajen shawo kan cutar Coronavirus, amma kuma ake gayyatar mutanen kasar Sin.

Dr. Faduyile ya ke cewa: “An yi katari, yawan mace-macen da aka samu a kasar Italiya ya karu sosai a daidai lokacin da Likitocin Sin su ka shiga kasar da sunan sun je bada gudumuwa.”

“Ko majalisar dinkin Duniya ta yabawa kokarin da Najeriya ta ke yi. Kin yabawa kokarin Malaman asibitinmu na gida ne a ce a wannan lokaci an gayyato Likitocin Sin.” Inji Faduyile.

Ita ma TUC ta bakin shugabanta da Sakatare na kasa, Quadri Olaleye da Musa Lawal-Ozigi sun ce ganin yadda ake fama da karancin masu cutar COVID-19, babu bukatar a kira Sinawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel