'Yan bindiga sun sace mai bawa gwamna Sule shawara, an kama daya daga cikinsu

'Yan bindiga sun sace mai bawa gwamna Sule shawara, an kama daya daga cikinsu

'Yan bindiga sun yi awon gaba da John Waje Mamman, mai bawa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, shawara a kan kananan hukumomi da raya karkara.

An sace Mamman a gidansa da ke garin Dari a karkashin karamar hukumar Kokona a daren ranar Asabar.

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa manema labarai cewa Mamman yana tare da abokansa a lokacin da 'yan bindiga suka kutsa cikin gidansa suka tafi da shi.

Ya bayyana cewa 'yan bindigar, wadanda aka gano cewa masu garkuwa da mutane ne, sun kewaye gidan Mamman tare da yin harbin iska domin tsorata jama'a.

'Yan bindiga sun sace mai bawa gwamna Sule shawara, an kama daya daga cikinsu
'Yan bindiga sun sace mai bawa gwamna Sule shawara, an kama daya daga cikinsu
Asali: Facebook

Shaidar ya bayyana cewa, sa'a ta kwacewa daya daga cikin 'yan bindigar a yayinda wasu matasa suka yi zafin nama suka damke shi.

DUBA WANNAN: An kubutar da mutane 54 daga wani haramtaccen gidan gyaran hali da ake wa mutane ukuba

Har ya zuwa lokacin da aka wallafa rahoto, babu wata sadarwa a tsakanin masu garkuwa da mutanen da iyalin Mamman.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kakakin rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya ce, "har yanzu babu wanda ya sanar da ofishin rundunar 'yan samu batun sace mai bawa gwamnan shawara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel