Kungiyar SERAP ta bukaci Gwamnati ta fadi yadda ake kashe kudin agajin COVID-19

Kungiyar SERAP ta bukaci Gwamnati ta fadi yadda ake kashe kudin agajin COVID-19

Kawo yanzu gwamnati ta na kokarin rage radadin da jama’a su ka shiga sakamakon cutar Coronavirus da ta barke, don haka ne ma aka fara rabawa wasu Marasa karfi kudi.

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna SERAP ta roki gwamnatin tarayyar Najeriya da babban bankin kasar na CBN su fadawa jama’a yadda ake kashe gudumuwar da ake tarawa.

Kungiyar SERAP ta na so gwamnatin Najeriya ta yi bayani dalla-dallar game da inda gudumuwar da Bayin Allah da Attajirai su ka tara domin yaki da annobar COVID-19, su ke shiga.

SERAP mai bin diddiki ta na so a bayyana sunayen wadanda aka ba kudi a matsayin tallafi na annobar da aka shiga. Wannan ne zai sa jama’a su san inda dukiyar kasar ta ke tafiya.

Wannan kungiya ta SERAP ta na son samun cikakken bayani game da wadanda aka ce an rabawa kayan abinci a Legas da Ogun inda aka hana fita saboda barkewar COVID-19.

KU KARANTA: A fito a wallafa sunayen wadanda aka ba kyautar N20, 000 - Sani

Har ila yau ta nemi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma CBN su fadi hanyar da ake bi wajen cigaba da daukar dawainiyar ciyar da ‘Daliban makarantun gwamnati.

A halin yanzu dai gwamnati ta rufe duk wasu makarantu domin rage yaduwar cutar Coronavirus. Duk da haka shugaba Buhari ya bada umarni a cigaba da ba ‘Dalibai abinci a inda su ke.

SERAP ta kuma bukaci a fito da sunayen duk wadanda aka ba kwangilar dafa abincin da ake rabawa ‘Yan makarantar, da bayani game da Garuruwan da su ka amfana da wannan tsari.

Kungiyar ta aika wannan roko ne a wata takardar FOI zuwa ga Ministar bada tallafi da agajin gagagawar Najeriya, Sadia Umar-Farouk da kuma gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele.

Takardar da SERAP ta aikawa CBN da Ministar ya nuna cewa idan har ba a fito da amsoshin da ake bukata ba, Lauyoyin kungiyar za su maka gwamnatin tarayya a gaban Alkali a kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel