Yan Abuja sun koka kan yadda ake gudunsu a garuruwansu na asali saboda Corona

Yan Abuja sun koka kan yadda ake gudunsu a garuruwansu na asali saboda Corona

Wasu jama’a na gudun mutanen da suka dawo jahar Adamawa daga Abuja da Lagas kan tsoron kamuwa da cutar covid-19 wacce aka fi sani da coronavirus.

Jahar Lagas da babbar birnin tarayya Abuja sune ka wajen yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 yayinda gwamnati ke fafutukar ganin ta hana yaduwar cutar.

Ali Kaka, wani abokin Mohammed Atiku, dan tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya kamu da cutar a kwanakin da suka gabata, ya ce ya cika da mamaki a lokacin da wasu tawagar abokansa suka tarwatse a lokacin da ya doshe su yan kwanaki bayan ya dawo daga Abuja.

Ya ce an yada jita-jita a fadin Yola cewa ya hadu da Muhammed Atiku a Abuja, wanda hakan ya sa mutane ke gudun hada inuwa dashi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yan Abuja sun koka kan yadda ake gudunsu a garuruwansu na asali saboda Corona
Yan Abuja sun koka kan yadda ake gudunsu a garuruwansu na asali saboda Corona
Source: Facebook

“Wallahi, ban hadu da Muhammed ba a Abuja ko kadan. Ganinmu na karshe dashi tsawon watanni uku da suka gabata ne kuma a nan Yola ne, amma wasu mutane sun yada jita-jita domin batar da jama’a.

“Tabbass, Muhammed Atiku abokina ne amma bamu hadu dashi ba a zuwan da nayi Abuja na karshe. Da ace mun hadu dashi, zan nemi a gwada ni saboda ina so na kasance cikin koshin lafiya,” in ji shi.

Kan haka, Kaka ya sha alwashin daukar matakin doka idan ya gano tushen jita-jitan domin ya zama darasi ga masu tsegumin.

Wasu daga cikin abokan Kaka sun ce da fari sun yarda da jita-jitan sannan suka kaurace masa saboda sun ji cewa ya halarci wani taro tare da Atiku Abubakar, sannan cewa ba za su iya wargi da lafiyarsu ba.

Wani mutum kuma da ya dawo daga Abuja, Musa Ine, ya yi korafi kan yadda makwabta da abokansa suka dunga yi masa, cewa mutane na ta kaurace masa tare da gulma a kansa ba tare da wani dalili ba.

“Sai na gano wani rade-radi da ke yawo, cewa na hadu da wasu manyan mutane a Abuja wadanda suka riga suka kamu, don haka mutane suka ki zuwa kusa dani. Na je waji shago siyan abubuwa, sai wani abokina ya yi gaggawan barin shagon ba tare da ya yi mun magana ba,” in ji shi.

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jahar Adamawa ya sanya dokar hana zirga-zirga a jahar, inda ya haramta tafiya na jaha-jaha duk a matakan hana yaduwar cutar a jahar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel