Coronavirus ta kashe tsohon shugaban kasar Congo

Coronavirus ta kashe tsohon shugaban kasar Congo

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, Jacques Joaquim Yhombi-Opango, ya mutu a birnin Paris sanadiyar cutar coronavirus.

Tsohon Shugaban kasar ya mutu ne yana da shekara 81 a duniya. Iyalansa sun ce da ma yana fama da rashin lafiya kafin ya kamu da coronavirus.

Mista Yhombi-Opango ya yi shugabancin Congo-Brazzaville daga 1977 har lokacin da shugaban da ke mulki yanzu Denis Sassou Nguesso ya kifar da gwamnatinsa a 1979.

Coronavirus ta kashe tsohon shugaban kasar Congo
Coronavirus ta kashe tsohon shugaban kasar Congo
Asali: UGC

Ya kwashe shekaru da dama a gidan yari kafin a kaddamar da tsarin jam'iyyu da dama a 1991 inda ya zama firai minista har zuwa lokacin da yakin basasa ya barke a 1997.

Ya tafi gudun hijira a kasar Faransa, ko da yake an kyale shi ya koma kasarsa shekara 10 bayan haka.

A wani labari na daban, mun ji cewa Amurkan da ke cikin Najeriya za su koma kasarsu. Ofishin Jakdancin Amurka da ke Legas ya shaidawa Duniya haka a farkon makon nan.

Kasar Amurka ta tanadi jiragen sama na musamman da za su dauke mutanenta daga Najeriya. Kasar ta dauki wannan mataki ne sabili da barkewar COVID-19.

Jawabin ya nuna cewa jiragen saman za su tashi kai-tsaye ne daga babban filin sauka da tashin jiragen saman Najeriya na Murtala Muhammed da ke Garin Legas.

Jakadancin kasar ta Amurka ta fitar da wannan bayani a shafinta na yanar gizo. Amurka ta ce ta na kokarin kai wani jirgin filin Nnamdi Azikiwe da ke Garin Abuja.

Hukumomin na Amurka sun fadawa mutanensu cewa su tafi filin jirgi da zarar sun samu wasikar da ke tabbatar da cewa sun samu wuri a jirgin saman da zai dauke su.

Har ila yau, wannan jawabi da ofishin Jakadancin Amurka ta yi, ya nuna cewa ba za a bar wadanda ba su samu wannan takarda su shiga filin jirgin saman ba.

Jiragen za su tashi ne daga Garin Ikeja zuwa babban filin jirgin saman nan na Washington-Dulles da ke Garin Virginia a cikin babban birnin Amurka na Washington DC.

Ana sa ran wannan jirgi zai isa Amurka a cikin makon nan bayan ya dauki ‘Yan kasar. A jiya mu ka ji cewa za a dauke ‘Yan kasar Israila da ke zaune a cikin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel