Coronavirus: Gwamnatin Nijar ta daukewa talakawa biyan kudin wuta da ruwa

Coronavirus: Gwamnatin Nijar ta daukewa talakawa biyan kudin wuta da ruwa

Daga cikin matakan hana yaduwar cutar Coronavirus wacce ta addabi duniya baki daya, gwamnatin kasar Nijar ta hana fita daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 ba safe a birnin Yamai inda a nan ne cutar ta fi tsanani.

Har ila yau gwamnatin ta hana shiga da fita daga birnin na tsawon makonni biyu daga ranar 28 ga watan Maris.

Shugaban kasar ta Nijar, Mohamadou Issoufou ya kuma bayar da umurnin soma farautar mutanen da ake zargin suna dauke da cutar a duk inda suke, don yi masu gwaji a cibiyoyin kiwon lafiya na cutar.

Coronavirus: Gwamnatin Nijar ta daukewa talakawa biyan kudin wuta da ruwa
Coronavirus: Gwamnatin Nijar ta daukewa talakawa biyan kudin wuta da ruwa
Asali: UGC

Hakazalika a kokarinta na sama wa jama’a sauki wajen samun kayayyakin da ake amfani da su wajen tsafta da kuma kashe kwayar cutar ta covid-19, gwamnatin ta soke haraji a kan irin wadannan kayayyaki da ake shiga da su kasar daga kasashen ketare, shafin labarai ta RFI ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma dauki sabbin jami’an kiwon lafiya 1500 don taimakawa wadanda ake da su a kasar a wannan hali da ake ciki.

Lura da yadda wannan cuta ta shafi harkokin yau da kullum da kuma na tattalin arziki kuwa, shugaba Issoufou, ya sanar cewa gwamnati za ta biya wa al’ummar kasar baki daya wutar lantarki da ruwan da za su yi amfani da su a watannin Afrilu da Mayun wannan shekara.

KU KARANTA KUMA: Rawar da coronavirus za ta taka a shari'ar da Dino ya shigar da Adeyemi

Wani sassaucin da gwamnatin kasar ta Nijar ta yi wa al’umma shi ne dakatar da karbar haraji kowane iri har sai cikin watan yuni mai zuwa, yayinda za a kaddamar da wani shirin raba wa jama’a marasa karfi abinci a matsayin kyauta, yayin da za a bullo da wani shirin sayar da abinci a kan farashi mai rahusa ga al’umma.

A wani labari na daban, mun ji cewa a yammacin yau, Lahadi, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai gabatar da jwabi kai tsaye ga 'yan Najeriya, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta bayyana.

A wani sako da Bashir Ahmad, mataimaki na musamman ga shugaba Buhari, ya fitar a shafinsa na tuwita, ya bayyana cewa shugaban kasar zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7:00 na yamma.

Ya bayyana cewa za a iya sauraro ko kallon jawabin na shugaba Buhari a gidajen radiyo da talabijin da ke fadin kasar nan, musamman gidajen talabijin da radiyo mallakar gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng